Gwamnan APC Ya Shirya Liyafa Bayan Nasara a Kotun Koli, Ya Aike da Muhimmin Saƙo Ga Bola Tinubu

Gwamnan APC Ya Shirya Liyafa Bayan Nasara a Kotun Koli, Ya Aike da Muhimmin Saƙo Ga Bola Tinubu

  • Gwamnan Ebonyi ya godewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, bayan samun nasara a kotun koli
  • A wurin wata liyafar murna ranar Lahadi, Gwamna Nwifuru ya tabbatarwa al'ummar jihar cewa zai musu hidima cikin gaskiya da ƙauna
  • Jihar Ebonyi na ɗaya daga cikin jihohin da kotun koli ta yanke hukuncin ƙarshe kan kararakin zaben gwamnoninsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ebonyi - Gwamna Francis Nwifuru ya godewa Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa tabbatar da tsarin doka da oda bayan ya samu nasara a hukuncin kotun ƙoli.

Kotun kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Gwamna Nwifuru, ɗan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar APC a zaman yanke hukunci ranar Jumu'a, 12 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Bwala: Hadimin Atiku ya faɗi abu 1 da zai yi idan Shugaba Tinubu ya naɗa shi muƙami a gwamnati

Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru.
Ebonyi: Gwamna Nwifuru Ya Godewa Shugaba Tinubu Kan Nasarar Da Ya Samu a Ƙotun Koli Hoto: @FrancisNwifuru
Asali: Facebook

Bisa haka gwamnan ya ƙara godewa Tinubu tare da jaddada alƙawarinsa na yi wa al'umma hidima da kuma cika masu muradansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Nwifuru ya ɗauki wannan alƙawarin ne a ɗakin taro da ke sabon gidan gwamnatinsa a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi ranar Lahadi.

Da yake jawabi a ɗakin taron yayin liyafar nasarar da ya samu a kotun ƙoli, Gwamnan na APC ya ce zai jagoranci al'ummar Ebonyi cikin gaskiya da ƙauna.

Kalaman Gwamna Nwifuru a wurin liyafa

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter, Gwamna Nwifuru ya ce:

"Ina godiya ga Allah bisa nasarar da ya bamu a kotun koli. Ina matukar godiya ga daukacin mutanen Ebonyi bisa goyon bayan da suka bamu da addu'o'i. Masu ruwa da tsaki ina godiya.

Kara karanta wannan

Yadda shugaban kasa Tinubu ya taka rawa a hukuncin Kotun Koli na zaben gwamnonin Kano da Plateau

"Alkawari na ne na ci gaba da yi muku hidima, mutanen Ebonyi, cikin gaskiya da kauna. Bangaren shari'a na ƙasar nan ya tsayu kan gaskiya da adalci, na godewa alkalai da suka jajirce kan gaskiya.
"Ga ubanmu kuma jagoranmu, mai girma shugaban kasa, Bola Tinubu, kwamandan asakarawan Nijeriya, ina gode maka da ka tsare tsarin dimokuradiyya, adalci, da zaman lafiya.”

Hadimin Atiku ya nuna sha'awar aiki da Tinubu

A wani rahoton kun ji cewa Duk da sukar da yake sha, Daniel Bwala ya tsaya kan bakarsa cewa a shirye yake ya bai wa gwamnatin Shugaba Tinubu gudummuwa.

Bwala, jigon PDP ya yi ƙarin haske kan ziyarar da aka ga ya kaiwa Bola Tinubu a Villa da kuma yiwuwar ba shi muƙamin gwamnati.

Asali: Legit.ng

Online view pixel