Murna Ta Koma Ciki Bayan Kotu da Datse dan PDP Shiga Takarar Sanata Saura Kwanaki 2 Zabe

Murna Ta Koma Ciki Bayan Kotu da Datse dan PDP Shiga Takarar Sanata Saura Kwanaki 2 Zabe

  • Ana saura kwanaki biyu a gudanar da zaben cike gurbi, kotu ta dakatar da dan takarar sanadan PDP a Ebonyi
  • Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dakatar da Silas Onu kan kin sanar da INEC taron jami'yyar kan zaben fidda gwanin
  • A martaninshi, Onu ya ce wannan hukunci an yanke shi ne don ta da rudani ganin saura kwanaki biyu kacal a gudanar da zaben

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta dakarar da dan takarar Sanata daga tsayawa takara.

Silas Onu dan jam'iyyar PDP shi ke neman kujerar Sanata a a zaben cike gurbi da za a yi a jihar Ebonyi.

Kara karanta wannan

An shiga rudani a Jos bayan Hukumar INEC ta cire sunan PDP a zaben cike gurbi, APC da LP sun shiga

Kotu ta dakatar da dan PDP tsayawa takara a zabe
Silas Onu ya hadu da tasgaro kan tsayawa takara. Hoto: Kotun Tarayya.
Asali: UGC

Wane hukunci kotun ta yanke?

Yayin yanke hukuncin, Mai Shari'a Ngajiwa ya ce PDP ta gaza sanar da hukumar zabe tun kwanaki 21 na taron jam'iyyar kafin zaben cike gurbin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan hukuncin na zuwa ne ana saura kwanaki biyu kacal a gudanar da zaben a fadin kasar, cewar Tribune.

Da ya ke martani kan hukuncin, Onu ya ce an yi hakan ne don kawo rudani ganin saura kwanaki biyu a gudadar da zabe.

Martanin dan takarar Sanatan a PDP

Silas ya bukaci magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu inda ya ce zai tsaya a zaben kuma zai daukaka kara, kamar yadda The Sun ta tattaro.

Ya ce:

"A yau, mun samu hukunkin mai shari'a Ngwajiwa da ke Babbar Tarayya cewa PDP ba ta sanar da INEC ba kwanaki 21 na taron jam'iyyar kan zaben cike gurbi.

Kara karanta wannan

Bayan sha da kyar a Kotun Koli, Gwamnan Arewa ya dage zaben ciyamomi kan dalili 1, bayanai sun fito

"Abin dubawa shi ne INEC na Abakaliki ne ta ke korafin rashin sanar da ita yayin da REC din hukumar da gan-gan ya ki halartar taron duk da sanar da ita.

An cire sunan PDP a zaben cike gurbi

A wani labarin, hukumar INEC ta cire tambarin PDP a takardar dangwala hannu na zaben cike gurbi a Plateau.

Wannan lamari ya tayar da hankalin jami'yyar inda suka nuna kin amincewarsu sa hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel