Kotun Musulunci Ta Aika Murja Kunya Zuwa Kurkuku a Kano, An Bayyana Dalili
- Bayan gurfanar da Murja Ibrahim Kunya a kotu, ana samun labari cewa an bada umarnin tsare ta
- Alkalin kotun musulunci ya amince a cigaba da tsare ‘Yar Tik Tok bisa zargin koyar da karuwanci
- Hukumar Hisbah tana zargin wanda ake kara da yin abin da zai tada hankalin mutane a jihar Kano
Kano - Bayan sauraron karar da aka shigar a kan Murjanatu Ibrahim Kunya, rahoto ya zo cewa alkali ya daure ta.
Aminiya ta fitar da labari a yammacin Talata alkalin kotun musulunci ya yi umarni a tsare Murja Ibrahim Kunya.
Murja Kunya a gidan gyaran hali
Za a rike wannan fitacciyar mata ne a gidan gyaran hali bisa zargin da ake yi mata na laifin koyar da karuwanci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Baya ga haka ana zargin Murja Kunya wanda tayi suna a dandalin Tik Tok da tada hankalin al’umma a jihar Kano.
A dazu ne aka ji Hukumar Hisbah ta Kano ta ce za tayi shari’a da Murja Kunya saboda zargin badalar da ta ke yi.
Matsayar Hisbah a kan Murja Kunya
Rundunar Hisbah ta ce mutanen unguwa suka kawo korafi a kan irin danyen aikin da wannan mata ta ke aikatawa.
Daga cikin zargin da ake yi mata akwai koyar da mutane karuwanci da tada hayaniya duk da an gargade ta.
Ba wannan ne karon farko da aka gurfanar da Murja Kunya a kotu ba, an taba yanke mata hukuncin yin laifi a baya.
An dade ana tuhumar wannan Baiwar Allah da yin abubuwan da su ka ci karo da al’adar Kano da tarbiyyar musulunci.
Saboda haka Aminu Daurawa ya zauna da ita kwanaki domin ganin ta tuba, wannan bai hana a koma gidan jiya ba.
An saki Murja Kunya?
Legit ta lura wasu su na yada cewa har an fito da Murja, kuma ta cigaba da abubuwan da ta saba a dandalin Tik Tok.
Rahotan da muka samu daga gidan rediyon Express ya nuna za a tsare ‘yar Tik Tok din kafin a kammala shari’a.
A babin siyasa, an ji labari Garba Kore ya ce son zuciya ya jawo Abdullahi Ganduje ya nada a sarakuna a jihar Kano.
Idan har Ali Baba ya bada shawara aka tsige Sarkin Kano, Garba Kore ya ce kyau a dawo da Muhammadu Sanusi II.
Asali: Legit.ng