Tsadar Rayuwa: Yadda Hukumar DSS Ta Tsare Malamin Addinin Musulunci a Kaduna Kan Caccakar Tinubu

Tsadar Rayuwa: Yadda Hukumar DSS Ta Tsare Malamin Addinin Musulunci a Kaduna Kan Caccakar Tinubu

  • Jami'an hukumar DSS ta gudanar da tambayoyi kan malamin addinin Musulunci da ke Zaria, Sheikh Auwal Sharrif kan sukar Tinubu
  • Malamin ya amsa tambayoyin ne bayan kwatanta mulkin Buhari da Tinubu kamar na Fir'auna da Hamana a Najeriya
  • Ya caccaki Tinubu ganin yadda ya dauki matakin gaggawa wurin cire tallafin mai wanda ya kara jefa mutane cikin kunci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna – Hukumar tsaro ta DSS ta tsare babban malamin Musulunci a Zaria da ke jihar Kaduna saboda kushe matakan Tinubu.

Malamin mai suna Sheikh Auwal Sharrif ya shiga hannun hukumar ce bayan ya kwatanta mulkin Tinubu da na Buhari kaman na Fir’auna da Hamana.

Kara karanta wannan

‘Yan Najeriya na shan wahala a mulkin nan ne saboda danyen aikin Buhari – Sanatan APC

Malamin addinin Musulunci ya sha tambayoyi a hukumar DSS bayan caccakar Tinubu
Hukumar DSS Ta Tisiye Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Sharrif a Kaduna Kan Caccakar Tinubu, Hoto: Bola Tinubu, Muhammdu Buhari.
Asali: Facebook

Mene ake zargin Malamin da aikatawa?

Daily Nigerian ta bayyana cewa hukumar ta kawo malamin ofishinta ne don matsar bayanai bayan ya caccaki gwamnatin Tinubu kan halin da ake ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gayyaci malamin ne a ranar Juma’a 9 ga watan Faburairu inda ya soki Tinubu yayin gabatar da huduba inda kuma aka sako shi a ranar.

Yayin hudubar, Sheikh Auwal ya bayyana tsarin shugabancin Buhari da na Tinubu kamar na Fir’auna da Hamana.

Ya caccaki Tinubu ganin yadda ya dauki matakin gaggawa wurin cire tallafin mai wanda ya kara jefa mutane cikin kunci, cewar Daily Independent.

An sako malamin bayan amsa tambayoyi

Wata majiya ta tabbatar da cewa an umarci kama malamin ne daga birnin Tarayyar Najeriya, Abuja amma an gudanar da tambayoyin ne a ofishin hukumar da ke Kaduna.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Sanatan Kano ya yi magana kan matakan da Tinubu ke dauka, ya yi alkawari a bangarensa

Majiyar ta tabbatar da cewa:

“Ya je shi inda ya amsa tambayoyi daga bisani an sake shi zuwa gida.”
“Daga abin da muka samu, an umarci kama malamin daga Abuja amma a ofishin hukumar da ke Kaduna aka gudanar da binciken.”

DSS ta sako Oscar bayan amsa tambayoyi

A baya, Kun ji cewa hukumar DSS ta matse daraktan fina-finan Kannywood, Sunusi Oscar kan furka wasu kalaman barazanar kisa.

Hukumar ta tsare daraktan ne bayan nadar wata murya da aka yi ya na kalaman barazanar ga wani jigo a gwamnatin Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.