Zanga-Zanga Ta Barke a Abuja, Hotuna da Bidiyo Sun Bayyana

Zanga-Zanga Ta Barke a Abuja, Hotuna da Bidiyo Sun Bayyana

  • Ma’aikatan jinya da unguwar zoma sun gudanar da zanga-zanga a Abuja don nuna rashin amincewa da sabbin ƙa’idojin tantance satifet da hukumar NMCN ta fito da su
  • Ma’aikatan jinya sun ce sabbin dokokin wani yunƙuri ne na daƙile ƴancin da suke da shi na neman damarmaki idan sun samu
  • Masu zanga-zangar sun buƙaci hujumar da ta magance matsalolin da suka shafi jin daɗinsu da suka haɗa da ƙarancin albashi, ƙarancin ma'aikata, da sauran haƙƙoƙinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ma’aikatan jinya a ƙarƙashin ƙungiyar ma’aikatan jinya da unguwar zoma ta ƙasa reshen Abuja, sun fara zanga-zanga.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, zanga-zangar an gudanar da ita ne kan sabbin ƙa'idojin tantance satifiket da hukumar Nursing and Midwifery Council (NMCN) ta fitar.

Kara karanta wannan

Remi Tinubu ta kai wa Sarkin Kano ziyara, bidiyon ya fito

Ma'aikatan jinya sun yi zanga-zanga a Abuja
Ma'aikatan jinya sun gudanar da zanga-zanga a Abuja Hoto: Wikus de Wet
Asali: Getty Images

Jaridar Vanguard ta ce zanga-zangar ta faru ne a ofishin NMCN da ke Abuja a ranar Litinin, 12 ga watan Fabrairun 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ma’aikatan jinya da unguwar zoman sun yi ta rera waƙoƙi da baje ɗaga alluna a kusa da harabar ginin hukumar.

Menene dalilin yin zanga-zangar?

Ma’aikatan jinya suna ƙorafi kan abin da suka bayyana a matsayin yunƙurin hana su ƴancin yin aiki.

Suna neman hukumar ta magance matsalolin jindaɗin ma'aikatan jinya, yanayin albashi, ƙarancin ma'aikata, da sauran haƙƙoƙinsu.

Wasu daga cikin rubuce-rubucen da ke kan allunan na cewa:

"A magance rashin aikin yi tsakanin ma’aikatan jinya, a magance matsalar ma'aikatan jabu, a magance matsalar jin daɗin ma'aikatan jinya.
"#Ba mu yarda da sabbin ƙa'idodin tantancewa ba. A daina ba ma’aikatan jinya na Najeriya takaici, mun riga mun sha wahala sosai, a kare ma’aikatan jinya, a kare lafiya, NMCN, mun ce a’a ga ƙa’idojin tantancewa, NMCN, kar a rage ma’aikatan jinya" da sauransu.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Sarkin Musulmi ya samo mafita ga 'yan Najeriya

Ga wasu hotuna da bidiyo ƙasa:

An Yi Zanga-Zanga a Legas

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu mutane a jihar Legas sun fito domin gudanar da zanga zanga kan halin ƙuncin da ake ciki a ƙasar nan.

Masu zanga-zangar waɗanɗa mata ne da matasa sun yi kira ga Shugaba Tinubu da ya ɗauki domin yunwa ta yi yawa a ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel