Ana Fama da Tsadar Kaya: Mai Baro Ya Tsere da Buhun Shinkafar Wata Mata, Za a Yi Bikin 'Diyarta Ne

Ana Fama da Tsadar Kaya: Mai Baro Ya Tsere da Buhun Shinkafar Wata Mata, Za a Yi Bikin 'Diyarta Ne

  • Yayin da ake fama da tsadar rayuwa a kasar, wata mata ta hadu da sharrin masu daukar kaya a kasuwar Kwali dake babban birnin tarayya Abuja
  • Matar mai suna Talatu Yakubu ta siya buhun shinkafa da sauran kayan abinci sai ta daurawa mai baro domin ya kai mata su bakin hanya amma sai ya yi layar zana
  • A cewar matar wacce za ta aurar da diyarta a ranar Juma'a, ta tsaya siyan kayan miya ne lokacin da ta nemi mai daukan kayan ta rasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Babban birnin tarayya, Abuja - Ana cikin matsin rayuwa, wani mai sana'ar tura baro ya tsere da shinkafa rabin buhu mallakin wata mata a yankin Kwali dake babban birnin tarayya, Abuja.

Kara karanta wannan

Talaka zai ji a jikinsa sakamakon tashin kudin shigo da kaya da aka yi wa Kwastam

Lamarin ya afku ne kasa da mako guda bayan wani 'dan achaba ya tsere da buhun garin masara a yankin Abaji da ke birnin tarayyar kasar, Daily Trust ta ruwaito.

Mai baro ya sace kayan wata mata a kasuwar Kwali
An yi amfani da hoton don misali ne Hoto: Bloomberg / Contributor
Asali: Getty Images

Yadda mai baro ya tsere da kayan abinci a kasuwar Kwali

Matar da aka sacewa shinkafar mai suna Talatu Yakubu, wacce ta sanar da mutane faruwar lamarin a kasuwar Kwali a ranar Litinin, ta ce ta dauki mai baron ne domin ya tayata fitar da shinkafar da kayan miya zuwa bakin hanya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Acewarta, ta zo kasuwar ne sannan ta siya shinkafa mudu 30 da jakar Semovita da kayan miya gabannin bikin 'diyarta da za a yi a ranar Juma'a a kauyen Sheda.

Ta ce ta tsaya siyan kayan attarugu da timatir ne kusa da kofar fita kasuwar lokacin da mai baron ya yi batan dabo.

Kara karanta wannan

Uwar gidan Shugaba Tinubu ta yi ƙus-ƙus da matan gwamnoni a Aso Villa, bayanai sun fito

Sata ta zama ruwan dare a kasuwar Kwali da Abaji

An rahoto cewa babu mako da zai wuce ba tare da an samu rahoton ko 'dan achaba ko mai baro ya tsere da kayan abincin mutane ba a kasuwannin Kwali da Abaji.

Jaridar ta kuma rahoto cewa an yi wa wani mai baro dukan kawo wuka bayan ya yi kokarin tserewa da kayan abincin da wata mata ta siya a kasuwar Kwali a makon jiya.

Kaya sun yi tsada a kasuwa

A wani labarin, mun ji cewa ana kukan wayyo Allah a fadin Najeriya sakamakon mugun tsadar kaya a kasuwa.

Baya ga tsada da ake fama da ita, a kullun ana samun sauyawar farashin kaya lamarin da ya jefa mutane cikin zullumi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel