Kogi: An Tsinci Gawar Daliban Kwaleji a Dakin Kwanansu, an Gano Abin da Ya Kashe Su

Kogi: An Tsinci Gawar Daliban Kwaleji a Dakin Kwanansu, an Gano Abin da Ya Kashe Su

  • Wasu dalibai biyu da ke karatu a kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kogi sun gamu da ajalinsu yayin da suke barci
  • Rundunar 'yan sanda a jihar sun tabbatar da cewa shaƙar hayakin dake fitowa daga janareta ne ya yi sanadin ajalin daliban
  • An ruwaito cewa an ajiye janaretan yana aiki a kusa da tagar dakin kwanan daliban, wanda kuma ya kwantar da wani dalibi a asibiti

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kogi - Dalibai biyu na kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kogi, Lokoja sun mutu sakamakon shakar hayakin da ke fitowa daga janareta da ke kusa da tagar dakunansu.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP William Ovye Aya, ya tabbatar da hakan ga gidan talabijin na Channels a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

"Ku Riƙa Faɗin Alheri Kan Kasar Ku" Shugaba Tinubu ya aike da muhimmin saƙo ga 'yan Najeriya

Hayakin janareta ya halaka dalibai a Kogi
Daliban na kwance a dakunan kwanansu hayakin ya halaka su. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Ya bayyana cewa wani dalibi daya ya tsira kuma yana jinya a wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda hayakin janaretan ya halaka daliban

Daliban da suka rasa rayukansu sune; Bilkisu Tijjani Eleojo mai shekaru 20 da kuma Ibrahim Haliru mai shekaru 26, yayin daMercy Ojochegbe ke asibiti.

An ce an ajiye janaretan ne a kusa da tagar wadanda abin ya shafa, wadanda suka mutu kafin wayewar gari yayin da suke yin barci.

An ba da rahoton cewa wasu makwabta ne suka gano gawarwakin wadanda suka mutu a dakin da sanyin safiyar Alhamis.

Hayakin janareta ya halaka wani jariri a Ondo

Ko a baya Legit Hausa ta ruwaito maku yadda hayakin janareta ya kashe wani jariri dan wata biyar a karamar hukumar Owo, jihar Ondo.

An tattaro cewa iyayen jaririn sun sun kunna janaretan ne da daddare suka yi barci, wanda hayakin ya sumar da su, tare da halaka jaririn.

Kara karanta wannan

Mataimakin Bursar na jami'ar Kwara ya rasu yana kallon wasan Super Eagles da Afrika ta Kudu

Wata majiya ta ce mata da mijin sun siyo sabon janareto yan kwanaki kafin afkuwar lamarin kuma su ukun sun kwanta lafiya kalau a daren ranar.

A jihar Edo ma hayakin janareta ya kashe uwa da 'ya'ya 5

Idan muka tsallaka jiihar Edo, Legit Hausa ta ruwaito yadda hayakin janareta ya halaka wata mata da 'yayanta biyar.

Lamarin ya faru ne a unguwar Akpata da ke Egor, jihar Edo, kuma an ruwaito mijin matar na kwance a asibiti bayan suma daga hayakin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel