Betta Edu: Kakakin Majalisa Abbas Ya Yi Magana Akan Zargin Rashawa da Ake Yiwa Gbajabiamila
- Kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas, ya bukaci hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike kan zargin rashawa da ake yi wa Femi Gbajabiamila
- Ana zargin Gbajabiamila, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa da hannu a almundahanar da ake zargin Betta Edu ta aikata
- Sai dai Abba ya yi watsi da zargin da ake yi wa Gbajabiamila da cewa ba gaskiya ba ne, yayin da ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su daina yada labaran karya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
FCT, Abuja - Tajudeen Abbas, kakakin majalisar wakilai, ya bukaci hukumomin tsaro da su fara bincike kan zargin cin hanci da rashawa da ake zargin Femi Gbajabiamila, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ya aikata.
Abbas ya yi kiran ne a ranar Alhamis, 8 ga watan Fabrairu, yayin wani taron manema labarai kan halin da kasar ke ciki a Abuja.
Abbas ya magantu kan badakalar Gbajabiamila da Betta Edu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An zargi Gbajabiamila, tsohon kakakin majalisar, da laifin cin hanci da rashawa da ya shafi ministar jin kai da aka dakatar, Betta Edu, inji rahoton The Punch.
Da yake tofa albarkacin bakinsa kan wannan zargi, Abbas ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su daina yada labaran karya da kuma yin suka mai ma’ana don yi wa jami’an gwamnati adalci yadda ya kamata.
Ya bayyana cewa zargin da ake yi wa shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa na iya kawo cikas ga dimokuradiyyar kasar.
Kakakin majalisar ya aika sako ga yan Najeriya
Dan siyasar wanda haifaffen garin Zariya ne ya ce yawan bata sunan da ake yi a shafukan sada zumunta na iya kawo cikas ga mutuncin mutum ko kungiya.
Abbas ya ce Gbajabiamila daya ne daga cikin miliyoyin ‘yan Najeriya da ke fuskantar cin zarafi ta yanar gizo tare da kuma bata suna a kullum.
Majalisar wakilai ta umarci IGP ya kama gwamnan CBN
A baya Legit Hausa ta rahoto cewa kwamitin majalisar wakilai a kan kararrakin jama’a ya bada umurnin a kama Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso.
Majalisar ta kuma bayar da umarnin kama babban akanta janar na tarayya Oluwatoyin Madein da wasu shugabannin hukumomin gwamnati 17.
A cewar ‘yan majalisar, Cardoso da wasu 18 sun kasa amsa gayyatar da aka yi musu har sau hudu domin bayar da ba'asi kan yadda suke tafiyar da ofisoshin su.
Asali: Legit.ng