Shiru magana ce, caccakata a yanar gizo ba mafita bace - Fatima Ganduje-Ajimobi

Shiru magana ce, caccakata a yanar gizo ba mafita bace - Fatima Ganduje-Ajimobi

- Fatima Ganduje-Ajimobi tace shiru magana ce, kuma duk cin zarafin da za'a yi mata a yanar gizo ba zai dame ta ba

- Bayan tayi wata wallafa a shafinta na Instagram a ranar Laraba wanda ya jawo cece-kuce, ta mayar da wannan martanin

- Tace a kowacce jam'iyya take, ita dai 'yar Najeriya ce, don haka ta damu da damuwar Kasarta

Fatima Ganduje-Ajimobi, diyar gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ta ce cin zarafin ta da wasu ke yi a yanar gizo ba zai taba razanar da ita ba.

Kada a manta a ranar Laraba, 21 ga watan Agusta ne Fatima tayi wata wallafa a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Instagram, inda tace "Na yi dana- sanin zabar shugabanni marasa kishin kasa."

Bayan ta yi wannan wallafar ne da wasu awanni, sai gashi ta kara wata, inda tace, "Shiru ma magana ce."

Ga dukkan alamu mutanen da suka ga wallafar da tayi ta farko, sun yi ta caccakarta, inda suke cewa bai dace ta dinga kushe wadanda suke jam'iyya daya da mahaifinta ba.

Sakamakon wannan sukar da ta sha, sai tayi musu martani da cewa, ita fa duk cin zarafin da za su yi mata sam ba zai taba shafarta ba, saboda bata damu da siyasa ba, kasarta ce damuwarta.

Inda ta wallafa, "Shiru magana ce, ba ruwana da wata jam'iyya, ni 'yar Najeriya ce, kuma na damu da Kasata. Don haka cin zarafi na a yanar gizo ba zai yi aiki a kaina ba!"

KU KARANTA: EndSARS: Gwamnoni sun aike muhimmin jan kunne ga shugabannin al'umma

Shiru magana ce, caccakata a yanar gizo ba mafita bace - Fatima Ganduje-Ajimobi
Shiru magana ce, caccakata a yanar gizo ba mafita bace - Fatima Ganduje-Ajimobi. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

Shiru magana ce, caccakata a yanar gizo ba mafita bace - Fatima Ganduje-Ajimobi
Shiru magana ce, caccakata a yanar gizo ba mafita bace - Fatima Ganduje-Ajimobi. Hoto daga @Fateeajimobi
Asali: Instagram

KU KARANTA: Da duminsa: Channels TV ta koma aiki bayan sa'o'in da tayi a rufe

A wani labari na daban, bayan tabarbarewar harkokin tsaro sakamakon zanga-zangar rushe SARS, NECO sun dakatar da jarabawarsu da daliban ajin karshe na sakandare suke yi.

Jaridar THISDAY ta gano yadda hukumar shirya jarabawar ta umarci masu jarabawa da masu kula da su a ofisoshi daban-daban da su dakatar har sai sun bada wata sanarwa nan gaba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel