Ba a Gama Da Emefiele Ba Majalisa Ta Bayar Da Umarnin a Kamo Sabon Gwamnan CBN

Ba a Gama Da Emefiele Ba Majalisa Ta Bayar Da Umarnin a Kamo Sabon Gwamnan CBN

  • Majalisar wakilai ta bayar da umarnin a kamo gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Olayemi Cardoso
  • Kwamitin majalisar kan ƙorafe-ƙorafen jama'a shi ne ya bayar sa sammacin kamo Cardoso da Akanta Janar ta tarayya da wasu mutum 17
  • Kwamitin ya bayar da umarnin kamun ne bayan ya gayyace su har sau huɗu sun ƙi su amsa gayyatar da ya yi musu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Kwamitin majalisar wakilai kan ƙorafe-ƙorafen jama’a ya bayar da sammacin kama sabon gwamnan babban bankin Najeriya, Mista Olayemi Cardoso, Babban Akanta Janar ta Tarayya, Misis Oluwatoyin Madein, da wasu mutum 17.

Kwamitin ya bayar da sammacin ne saboda ƙin amincewa da gayyatar da kwamitin ya yi musu domin amsa tambayoyi game da ayyukansu, cewar rahoton Nigerian Tribune.

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ya yi magana kan kisan Musulmai a Kaduna

Majalisar wakilai ta bukaci a cafke gwamnan CBN
Majalisar wakilai ta nemi a kamo gwamnan CBN Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

An bayar da sammacin kamun ne saboda yadda suka cigaba da jajircewa wajen ƙin amsa gayyatar bayyana a gaban kwamitin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban Kwamitin, Micheal Irom, ya yanke hukuncin cewa Sufeto Janar na ƴan sanda ya tabbatar da bayyanar manyan shugabannin a gaban kwamitin a ranar 14 ga watan Disamba ta hanyar sammacin kamun.

Tun da farko yayin zaman kwamitin a ranar Talata, Fred Abedi ya gabatar da kudirin da ya kai ga amincewa da sammacin kamun.

Ɗan majalisar ya ce duk da gayyatar da aka yi musu har sau hudu, sun kasa halartar zaman kwamitin, lamarin da ya tilasta ɗaukar wannan matakin.

Majalisa ta shirya taron jin ra'ayin jama'a kan kasafin kuɗi

Majalisar wakilai ta An fara gudanar da taron jin ra'ayoyin jama'a kan kasafin kudin 2024 da shugaban kasa Tinubu ya gabatarwa majalisar dokokin tarayya a Abuja.

Kara karanta wannan

A Karshe, Jam'iyyar PDP ta fara ɗaukar matakan farfaɗowa daga bugun da ta sha a zaben 2023

Taron jin ra'ayin jama'an na gudana ne karkashin kwamitin majalisar kan kasafin kudi, da kuma sashen gudanar da taruka, na ofishin kakakin majalisar tarayya.

Majalisar Wakilai Ta Yi Sabbin Shugabannin Ƙwamitoci

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar wakilai ta yi gyara kan shugabancin kwamitoci 27 na majalisar.

Kakakin majalisar wakilan Tajudeen Abbas ya karanto sabbin shugabannin kwamitocin da mataimakansu. Kwamitocin sun kunshi guda 26 da ake da su a majalisar wakilai ta ƙasa da kuma ƙarin guda ɗaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel