Abubuwa 8 da ya kamata mu guji sanyawa a shafukan sada zumunta

Abubuwa 8 da ya kamata mu guji sanyawa a shafukan sada zumunta

Shafunkan sada zumunta sun riga da sun shiga rayuwar mutane a yanzu. Amma sai dai muna mantawa da wani abu guda daya, wannan abin kuwa shi ne ba komi ake turawa a shafukan sada zumunta.

Wani lokaci wasu mutanen na watsa sirrikansu a shafin sada zumunta wanda kuma bai kamata a ce duniya ta sani ba, kan kace kwabo ya zaga duniya saboda harka ce da ta shafi yanar gizo.

KU KARANTA:Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 5 a Yola

Saboda wannan dalilin ne muka tattaro maku wasu abubuwa guda takwas da ya kamata ku nisanci turawa a shafukan sada zumunta, ga su kamar haka;

1. Labarin karya ko jita-jita

A lokacin da ka tura da labarin karya ko kuma kake yada jita-jita, zaka iya tayar da hankali wani ta yadda idan akwai mai hawan jinni ba mamaki rashin lafiyarsa ya matso.

2. Hoton wata hira ta sirri da kayi tsakanin da wani/wata

Tunda kalmar sirri ta riga ta shigo ciki ai magana ta kare. Zaka iya samun mutane da yawa sun nuna jin dadin abinda kayi ta hanyar latsa ‘Like’ amma kuma babu wanda zai fada maka sirrinsa saboda kada ka fallasa shi.

3. Adireshen ka na gida

Saboda halin tsaro ya kamata ku kiyayi sanya adireshen wurin da kuke zama a shafunka sada zumunta. Akwai bata gari da yawa yanzu komai zai iya faruwa da kai sakamakon wannan abu.

4. Lambar wayarka

A yayin da kake son abokanka su samu damar kiranka a waya, akwai kuma miyagun mutane da za su iya amfani da lambar domin yi maka illa.

5. Yanayi samun kudinka

Kai biloniya ne ko miloniya ko kuma mai rufin asiri, wannan ba abu ne da zaka yada a shafukan sada zumunta ba saboda sirrin rayuwarka ne.

6. Bayanai na hakika game da kanka

A lokacin da ka wallafa wannan bayani a shafin sada zumunta jama’a da dama za su gani, ko da daga baya kayi shawarar sharewa kada ka manta nake ne kawai zaka iya sharewa amma banda wanda yake a wurin sauran mutane.

7. Ainihin wurin da kake a lokacin aika sakon

Wasu mutane ba su san idan mutum ya aika da sako a tuwita ko facebook yana fitowa da wurin da yake ba lokacin. Fitar wannan bayanin kan yia zame maka illa.

8. Duk abinda ba ka son ya kasance a yanar gizo har abada

A duk sanda ka tura da wani sako a shafunka sada zumunta, ka dauka kawai zai kasance a wurin ne har abada. A don haka kafin ka daura abu kayi tunani da kyau ka da ka yada sirrinka.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel