Shugaba Tinubu Zai Lula Zuwa Kallon Wasan Ƙarshe Na Gasar Cin Kofin Afirka AFCON? Gaskiya Ta Bayyana

Shugaba Tinubu Zai Lula Zuwa Kallon Wasan Ƙarshe Na Gasar Cin Kofin Afirka AFCON? Gaskiya Ta Bayyana

  • Hukumar CAF ta tabbatar da cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu zai halarci filin da za a buga wasan ƙarshe a Ivory Coast
  • Shugaban CAF, Patrice Motsepe, ya bayyana cewa an faɗa masa Tinubu zai zo kallon wasan ranar Lahadi, 11 ga watan Fabrairu, 2024
  • Tawagar Super Eagles ta Najeriya za ta kara da Ivory Coast mai masaukin baki, ƙasashen biyu sun fito ne daga rukuni ɗaya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Shugaban hukumar kwallon ƙafa ta nahiyar Afirka (CAF), Patrice Motsepe, ya tabbatar da cewa Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu zai je kallon wasan karshe na gasar AFCON.

Msita Motsepe ya bayyana cewa Shugaba Tinubu zai kalli wasan ƙarshe na cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) wanda za a yi ranar Lahadi, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

AFCPN 2023: Kocin Cote d'Ivoire ya fadi hanyar da za su bi don doke Najeriya a wasan karshe

Shugaba Tinubu zai je kallon wasan ƙarshe.
Tinubu zai kalli wasan karshe na AFCON a Ivory Coast, in ji shugaban CAF Hoto: Ajuri Ngelale, Super Eagles
Asali: UGC

Shugaban CAF ya bayyana haka ne a wurin taron manema labarai da ya gudanar ranar Jumu'a, 9 ga watan Fabrairu, 2024 sa'o'i 48 gabanin take wasan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tawagar ƴan wasan Najeriya Super Eagles za su murza leda a wasan ƙarshe na gasar AFCON karo na farko tun shekarar 2013 da suka lashe kofin.

Super Eagles ta tsallaka zuwa zagayen karshe na gasar bayan da ta doke Bafana Bafana ta ƙasar Afirka ta Kudu a bugun daga kai sai mai tsaron raga a wasan kusa da na karshe.

Tawagar ƴan wasan Najeriya za ta kara da Ivory Coast a filin wasa na Olympics, Ebimpe da ke Abidjan, ranar Lahadi da karfe 9 na dare agogon gida Najeriya.

Shin Tinubu zai je kallon wasan ƙarshe na AFCON?

Da yake tabbatar da lamarin, Motsepe ya ce an sanar da shi cewa Tinubu zai kasance a filin kwallon domin kallon wasan da Najeriya ke da burin lashe kofin AFCON na hudu.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 12 da ya kamata su sanni kan wasan Ƙarshe da Najeriya zata fafata da Ivory Coast

“An gaya mani cewa shugaban Najeriya zai zo (kallon wasan karshe). Na zauna a kusa da mataimakin shugaban kasar a lokacin da suke fafatawa da Afirka ta Kudu."

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya halarci filin wasan da Najeriya ta buga wasan daf da na ƙarshe a Bouake.

Abinda ya dace ku sani game da wasan ƙarshe na AFCON

A wani rahoton kuma mun tattaro muku abubuwa 12 da ya kamata ku sani game da wasan ƙarshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka AFCON.

Tawagar ƴan wasan Super Eagles ta Najeriya zasu fafata da tawagar Côte d’Ivoire a wasan ƙarshe domin tantance zakaran gasar AFCON 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262