Labari Da Dumi: Bola Tinubu Ya Rattaba Hannu a Sabuwar Dokar da Za Ta Canza Lantarki

Labari Da Dumi: Bola Tinubu Ya Rattaba Hannu a Sabuwar Dokar da Za Ta Canza Lantarki

  • Shugaban kasar Najeriya ya gama yin na’am da kudirin yi wa dokar wutar lantarki gyare-gyare
  • Kudirin ya zama doka bayan sanarwar sa hannun Bola Ahmed Tinubu a yammacin Juma’a
  • Ajuri Ngelale ya sanar da haka a wani jawabi na musamman da ya fitar daga fadar Aso Rock Villa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sa hannunsa a kudirin lantarki wanda hakan ya sa ya zama sabuwar doka.

A ranar Juma’a, Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu a fadar shugaban kasa, Ajuri Ngelale ya bada wannan sanarwa.

Bola Tinubu
Bola Tinubu ya sa hannu a dokar lantarki Hoto: @Dolusegun16, Getty
Asali: Twitter

Ngelale ya fitar da jawabi wanda yayi wa take da “Sa hannun shugaban kasa Tinubu ga kudirin (garambawul) da dokar lantarki."

Kara karanta wannan

An shiga rudani kan batun mutuwar babban basarake a Najeriya, an fadi gaskiyar abin da ya same shi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

The Guardian ta ce Honarabul Babajimi Benson ya fara kawo wannan kudiri da zai yi wa dokokin lantarki garambawul a majalisa.

Babajimi Benson mai wakiltar Ikorodu a majalisar wakilan tarayya ya kawo wasu jerin kwaskwarima da aka amince da su.

Jawabin ya ce dokar da aka kawo za ta inganta rayuwar yankunan da ke samar da wuta, daga nan sai a raba ta hannun DisCos.

Nairametrics take cewa dokar ta yarda a rika ware 5% na kudin da aka kashe a shekarar baya a kan garuruwan da ke samar da wuta.

Kamfanonin GENCOs masu samar da wuta za su rika taimakawa da kudi kamar yadda NDDC ta ke aiki a jihohi masu fetur.

Tinubu da sabuwar dokar wuta

Tun a shekarar bara, Bola Tinubu ya sa hannu a dokar lantarki ta 2023 wanda ta canji dokar wuta da ake amfani da ita tun 2005.

Kara karanta wannan

Zanga-zanga sun tada hankalin Gwamnati, Shugaban kasa ya dauki mataki a guje

Daga yanzu, jihohin kasar sun samu ikon bada lasisi ga duk ‘yan kasuwan da za su bude kananan tashohin makamashin wuta.

Dokar ta haramta raba wutar lantarki tsakanin jihohi da zuwa wata kasa daga yanzu.

Dangote a Kano

Mai kudin Afrika watau Aliko Dangote ya sha alwashin bada gudumuwa a mahaifarsa ta Kano kamar yadda labari ya zo.

Kamfanin Dangote zai gina asibitin masu cutar sikila kuma zai gina bangarori a asibitin Murtala bayan kiran Abba Kabir Yusuf.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng