Kotu Ta Ɗibawa Tinubu Wa'adin Kawo Karshen Matsalar Tsadar Rayuwa a Najeriya

Kotu Ta Ɗibawa Tinubu Wa'adin Kawo Karshen Matsalar Tsadar Rayuwa a Najeriya

  • Babbar kotun tarayya dake Legas ta umurci gwamnatin tarayya da ta kayyade farashin kayayyaki yayin da ake fama da tsadar rayuwa
  • Da yake bayar da umurnin a ranar Laraba, 7 ga watan Fabrairu, alkalin kotun ya bukaci gwamnatin Shugaba Tinubu ta aiwatar da umurnin cikin kwanaki bakwai masu zuwa
  • Haka zalika, Mai Shari'a Lewis-Allagoa ya umurci gwamnati ta kayyade farashin iskar gas, fetur da kalanzir

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Lagos - Wata babbar kotun tarayya dake zama a Ikoyi, Legas ta umurci gwamnatin tarayya da ta kayyade farashin kayayyaki da man fetur cikin kwanaki bakwai.

Mai shari’a Ambose Lewis-Allagoa ne ya bayar da umarnin a ranar Laraba, 7 ga watan Fabrairu, a wata kara da 'dan rajin kare hakkin dan Adam, Femi Falana SAN ya shigar, rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Dalibar aji 4 a jami'ar Najeriya ta dauki ranta da kanta, an gano dalili

Kotu ta umurci gwamnatin Tinubu da ta saita farashin kaya
Kotu Ta Umurci Gwamnatin Tinubu Ta Sanya Farashi a Kayayyaki Cikin Kwanaki 7 Hoto: NESG
Asali: Twitter

Wani umurni kotu ta bayar?

Kama yadda jaridar Daily Post ta ruwaito, Mai Shari'a Lewis-Allagoa ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wannan hukunci ne kan karar da Femi Falana ya shigar mai lamba FHC/CS/869/2023, inda ake ake karar, antoni janar na tarayya da hukumar kula da farashi ta kasa.
"Kotu ta gano cewa wadanda ake karar ba su mayar da martani kan wannan karar ba duk da cewa an aika masu da takardar karar."

Alkalin kotun ya ci gaba da cewa:

"Don haka ne wannan kotun, ta karbi dukkanin rokon da mai shigar da karar ya gabatar gaban kotun.
"Kotu na umurtar gwamnatin Najeriya ta kayyade farashin madara, fulawa, sukari, gishiri, kekuna, ashana, babura, motoci da kayayyakin gyaransu."

Alkalin ya umurci gwamnatin Najeriya da ta sanya farashin madara, garin pilawa, gishiri, sikari, keke, ashana, babur, mota da kayan fetur da suka hada da dizal, man fetur da kananzir.

Kara karanta wannan

AFCON: Ana saura kwana 4 aurensa ya rasu, cewar iyalan marigayi Ayuba a Kwara, bayanai sun fito

Legit Hausa ta zanta da wata mai sana'ar abinci a garin Minna, Hajiya Hadiza Bawa inda ta nuna goyon bayanta akan wannan umurni da kotu ta ba gwamnati tana mai cewa:

"Tun farko abin da ya kamata ace gwamnati ta yi kenan kafin a kai inda ake a yanzu. A bar 'yan kasuwa sakaka suna yin abin da suka ga dama, kawai sai su yi ta kara farashin abubuwa babu tunani.
"Ka duba jiya a kasuwar gwadabe N35000 aka siyar da kwandon tumatir, kada shinkafa ya ji labari. Ko mu da muke sana'ar abinci yanzu kawai dai muna yi ne amma ba wai don akwai wata riba ba.
"Wasu lokutan ma sai mutum ya sha fama kafin uwar kudin ya dawo. Idan har gwamnati ta kayyade farashin abubuwa da kanta za a samu saukin abun musamman ma daga wajen 'yan kasuwa masu cin buri da yawa."

Wani roko APC ta yi wa 'yan adawa?

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Ta yiwu Tinubu ya rufe iyakar Najeriya kan karancin abinci, ya fadi sauran hanyoyi

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar APC mai mulki ta bukaci jam’iyyun adawa da su bar korafi kan halin da kasar ke ciki a yanzu.

Jam’iyyar ta ce ya kamata su nemo hanyar taimakawa don tsame kasar a halin da a ke ciki madadin yawan korafe-korafe.

Kakakin jam’iyyar ta kasa, Felix Morka shi ya bayyana haka a jiya Talata 6 ga watan Faburairu yayin hira da Channels TV.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng