Tsadar Rayuwa: Gwamnan APC a Arewa Zai Rage Kudin Man Fetur Ga Manoma a Jiharsa, Bayanai Sun Fito

Tsadar Rayuwa: Gwamnan APC a Arewa Zai Rage Kudin Man Fetur Ga Manoma a Jiharsa, Bayanai Sun Fito

  • Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ya shirya karya farashin man fetur ga manoma don inganta noma
  • Zulum ya ce zai rage farashin mai din ne musamman don manoman Damasak da ke karamar hukumar Mobbar
  • Farfesa Zulum ya ce ya dauki matakin ne don inganta samar da abinci a jihar yayin da yankin ya sha fama da rashin tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Borno - Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya yi alkawarin rage kudin man fetur ga manoma a jihar.

Zulum ya ce zai rage farashin mai din ne musamman don manoman Damasak da ke karamar hukumar Mobbar a jihar, cewar BusinessDay.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya tono tushen matsalar ƴan bindiga a Arewa, ya jero hanyoyin magance su

Gwamnan Arewa zai rage farashin man fetur saboda manoma
Gwamna Zulum ya yi alkawarin rage farashin fetur saboda manoma a Borno. Hoto: Babagana Zulum.
Asali: Facebook

Mene Gwamna Zulum ke cewa kan manoma?

Gwamnan ya ce ya dauki matakin ne don inganta samar da abinci a jihar yayin da yankin ya sha fama da matsalar rashin tsaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Damasak na daga cikin garuruwan da ke samar da mafi yawan abincin jihar wanda ta sha fama da matsalar hare-haren Boko Haram.

Farfesa Zulum ya bayyana haka ne yayin taron rarraba kayan tallafi ga zaurawa da marasa karfi, cewar Daily Trust.

Gwamna Zulum ya yi alkawarin mayar da jihar wurin samar da abinci tare da dogaro da kanta a fannin abinci.

Ya ce:

"Don samar da abin dogaro ga mutanenmu, muna kokarin daukar matakai don inganta harkokin noma a jihar.
"Muna kuma kokarin rage wahalhalu ga manoma musamman a yankin Damasak.
"Ga manoman wannan yanki, babban hanyar gudanar da harkokinsu shi ne man fetur, zan yi kokarin kawo sauki a wannan bangare."

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano zai je ya samu Tinubu su yi kus-kus kan wata gagarumar matsala 1 tak

Ya kara da cewa:

"Gwamnati za ta samar da gidajen mai guda biyu da za su siyar da man cikin sauki ga manoman, wannan zai sa a siya a farashi mai sauki don ba da ruwa ga gonakinsu."

Bayan ba da man fetur mai sauki, Zulum ya yi alkawarin samar da injuna masu amfani da hasken rana da taki da iri da sauran kayan noma.

Zulum ya nada Wazirin Borno

Kun ji cewa Gwamna Babagana Zulum ya amince da nadin Mutawali Shettima Bukar a matsayin Wazirin Borno.

Wannan nadin na zuwa ne bayan da Shehun Borno, Abubakar Ibn Umar Al Amin El-Kanemi ya mika sunan Bukar ga gwamnan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel