Tsadar Rayuwa: Jam’iyyar APC Ta Roki Jam’iyyun Adawa Muhimmin Abu 1, Ta Ce Duk Tsarinsu Daya Ne

Tsadar Rayuwa: Jam’iyyar APC Ta Roki Jam’iyyun Adawa Muhimmin Abu 1, Ta Ce Duk Tsarinsu Daya Ne

  • Yayin da ake cikin mawuyacin hali a Najeriya, Jam’iyyar APC ta tura bukata ga jam’iyyun adawa a kasar
  • Jam’iyyar ta soki yadda jam’iyyun adawa ke kushe tsate-tsaren gwamnatin madadain kawo mafita
  • Kakakin jam’iyyar ta kasa, Felix Morka shi ya bayyana haka a jiya Talata 6 ga watan Faburairu yayin hira da ‘yan jaridu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Jam’iyyar APC mai mulki ta bukaci jam’iyyun adawa da su bar korafi kan halin da kasar ke ciki a yanzu.

Jam’iyyar ta ce ya kamata su nemo hanyar taimakawa don tsame kasar a halin da a ke ciki madadin yawan korafe-korafe.

Jam'iyyar APC ta tura sako ga jam'iyyun adawa kan tsadar rayuwa
Jam’iyyar APC ta ce duk jam'iyyun adawa a kasar tsarin Tinubu za su yi. Hoto: Atiku Abubakar, Bola Tinubu, Rabiu Kwankwaso.
Asali: Facebook

Menene APC ke cewa kan jam'iyyun adawa?

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga matar aure kan mutuwar 'dan kishiyarta a Kano

Kakakin jam’iyyar ta kasa, Felix Morka shi ya bayyana haka a jiya Talata 6 ga watan Faburairu yayin hira da Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Morka ya ce babban abin da ke damunsu shi ne yadda jam’iyyun adawa ke kushe ko wane tsarin gwamnati.

Ya ce ba haka adawa ta ke ba, ya kamata su rinka kawo gyara da shawarwari don dakile matsalolin kasar.

Shawarin da APC ta bai wa jam'iyyun adawa

Ya ce:

“Daga cikin abin da ke damunmu shi ne adawa ba wai kushe tsare-tsaren gwamnati ba ne, bai kamata ya tsaya a kushe wa ba.
“Wadanna shugabanni ya kamata su kawo wata mafita idan har su na da shi wanda gwamnati ba ta hararo ba.”

Felix ya ce jam’iyyun PDP da LP duk sun yi alkawarin daukar matakan da Tinubu ya ke dauka yanzu a lokacin kamfe, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Rigima ta ƙara tsananta a APC yayin da mutum 2 suka ayyana kansu a matsayin shugaban jam'iyya

Ya ce gwamnatin Tinubu ta na sane da dukkan wahalhalun da ‘yan kasar ke sha inda ya bukaci karin hakuri daga mutane.

Jam’iyyar APC ta zargi jam’iyyun adawa

Kun ji cewa jam’iyyar APC mai mulki ta zargi jam’iyyun adawa da daukar nauyin masu zanga-zanga.

Jam’iyyar ta na magana ne kan zanga-zangar da ta barke a biranen Minna da Kano a ranar Litinin 5 ga watan Faburairu.

Wannan na zuwa ne yayn da ake cikin wani irin mawuyacin hali a kasar na tsadar kayayyaki musamnan bangaren abinci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel