Mummunar Zanga-Zanga Ta Barke a Jihar Arewa Kan Yanayin Halin Kunci da Ake Ciki, Bayanai Sun Fito
- Zanga-zanga ta barke a birnin Minna da ke jihar Neja saboda tsadar rayuwa da ake ciki a fadin kasar baki daya
- Mutanen sun fito zanga-zangar ce a yau Litinin 5 ga watan Faburairu inda suka cika titunan birnin Minna
- Wannan na zuwa ne yayin da ake cikin mawuyacin halin matsain rayuwa da kuma tsadar kayayyaki musamman abinci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Neja – Mazauna birnin Minna da ke jihar Neja sun fito zanga-zangar nuna rashin jin dadi kan tsadar rayuwa a kasar.
Mutanen sun fito zanga-zangar ce a yau Litinin 5 ga watan Faburairu inda suka cika titunan birnin, cewar Channels TV.
Mene dalilin zanga-zangar a Minna?
Masu zanga-zangar da suka hada da mata da matasa sun cika titunan birnin tare da rera wakoki yayin da jami’an tsaro ke kallonsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matasan suka ce tsadar rayuwa a kasar musamman kayayyakin abinci da kuma rashin yin wani abu kan lamarin shi ne dalilin zanga-zangar.
Suka ce sun dauki matakin yin zanga-zangar ce don gwamnati ta ji kukansu tare da daukar matakin dakile matsalar.
Martanin gwamnatin jihar kan wannan lamari
Mataimakin gwamna jihar, Yakubu Garba yayin jawabi ga masu zanga-zangar ya ce suna sane da halin da ake ciki, cewar Daily Post.
Ya ce duk wata wahala da jama'ar kasar ke fama da shi sun sani inda ya ce su na duk abin da ya dace don dakile matsalar.
Har ila yau, ya ce akwai wasu matakai da ake da su a kasa don rage hauhawan farashin kayayyaki dalilin cire tallafin man fetur.
Ministan Tinubu ya fadi alfanun cire tallafi
Kun ji cewa, Ministan yada labarai a Najeriya, Mohammed Idris ya bayyana alkarin da ke cikin cire tallafin mai a kasar.
Idris ya ce da kudaden da ake samu bayan cire tallafin ne ake amfani da su wurin ayyukan raya kasa a Najeriya.
Ya ce da ba a cire tallafin ba da wahalar da za a shiga sai ta fi wanda ake ciki yanzu a kasar.
Asali: Legit.ng