An Shiga Rububi, Gwamnatin Tinubu Ta Magantu Kan Yadda Za Ta Daga Darajar Naira a Kan Dala

An Shiga Rububi, Gwamnatin Tinubu Ta Magantu Kan Yadda Za Ta Daga Darajar Naira a Kan Dala

  • Gwamnatin tarayya na ta fara daukar kwararan matakai na tabbatar da farfado da darajar Naira don gogayya da sauran kudaden duniya
  • Ministan yada labaran kasar ya bayyana cewa, gwamnati ta dukufa wajen aiwatar da tsare-tsaren tattalin arziki don shawo kan matsalar
  • Ya ce sauye-sauyen da gwamnatin ke shirin yi za su kawo ci gaba wajen shawo kan hauhawar farashin kayayyaki da daidaitar farashi a kasar

Salisu Ibrahim ne babban editan (Copy Editor) sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Neja - A martanin gwamnati ga faduwar darajar Naira da ake ci gaba da gani a kasuwar canji, Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin yin gyare-gyare a fannin tattalin arziki domin dawo da darajar kudin kasar.

Kara karanta wannan

Yobe: Mayakan Boko Haram sun kai hari a cibiyar tattara sakamakon zabe, sun kashe mutum 2

Mohammed Idris, ministan yada labarai na kasa ne ya bayyana hakan a yayin taron makon manema labarai na kungiyar ‘yan jarida reshen jihar Neja (NUJ) na shekarar 2024 a Minna ranar Asabar.

Tinubu zai farfado da darajar Naira, ya fadi ta yaya
Za a farfado da darajar Naira, Tinubu ya magantu | Hoto: StateHouse, MoneyMarket
Asali: UGC

Idris ya jaddada aniyar gwamnatinsu na aiwatar da sauye-sauyen da suka shafi inganta ci gaban tattalin arziki, shawo kan hauhawar farashin kayayyaki, rage tsadar rayuwa da daidaita kasuwar musayar kudi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane sauyi aka samu a baya?

A cikin ‘yan watannin da suka gabata, Naira ta fuskanci koma baya ainun a kasuwar canji a hukumance da kuma wanda ba a hukumance ba, The Nation ta ruwaito.

Koma bayanta a makon da ya gabata ya N1,400/$ a halastacciyar kasuwa da kuma sama da N1,500/$ a kasuwar bayan fage.

Sai dai, tsarin da babban bankin kasar ya zo dashi na kokarin magance matsalar da alamu ya fara daukar seti, domin an fara ganin sauyi da saukar farashin dala idan aka kwatanta da Naira.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Katsina ta dauki gagarumin mataki bayan 'yan bindiga sun kwashe 'yan kai amarya 60

Meye gwamnatin Tinubu ke shirin yi?

A rahoton BluePrint, ministan ya kara da cewa:

“Gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da aiwatar da sauye-sauye a fannin tattalin arziki don cimma manyan manufofin tattalin arziki na dauwamar ci gaban tattalin arziki.
“Sauyin zai kawo raguwar hauhawar farashin kayayyaki, da saukaka tsadar rayuwa, da daidaita musayar kudaden waje da samar da ayyukan yi da dai sauransu.”

Ta yaya za a farfado da darajar Naira?

A wani labarin, Reno Omokri ya bayyana hanyar da za a bi wajen tabbatar da an dawo da kimar Naira a daidai wannan lokacin.

Tsohon hadimin na tsohon shugaban kasa Jonathan ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter, inda ya tuna da yadda tsarin yake a baya.

A halin yanzu, 'yan Najeriya na ci gaba da kuka kan yadda farashin kayayyaki da kuma hauhawar dala a kasuwar canji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel