Ministar Matasa Ta Magantu Kan Karawa Matasa Masu Yi Wa Kasa Hidima Alawus Daga Naira 33,000

Ministar Matasa Ta Magantu Kan Karawa Matasa Masu Yi Wa Kasa Hidima Alawus Daga Naira 33,000

  • Gwamnatin tarayya tana nazarin kudin da take warewa hukumar NYSC da ke biyan matasa masu yi wa kasa hidima alawus a wata-wata
  • Ministar matasa, Jamila Bio-Ibrahim, ta bayyana hakan a ranar Lahadi, 4 ga watan Fabrairu, yayin tattaunawa da gidan talabijin na Channels TV
  • Ibrahim Hamisu da Mufidat Muhammad sun roki gwamnati ta gaggauta karawa 'yan bautar kasa alawu, sun zanta da Legit Hausa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

FCT, Abuja – Jamila Bio Ibrahim, ministar matasa ta Najeriya, ta ce ba ta da tabbas ko gwamnatin tarayya za ta kara alawus din da ake ba matasa masu yi wa kasa hidima.

Bio Ibrahim ta bayyana hakan ne a lokacin da take jawabi a shirin 'Siyasar Lahadi' na gidan talabijin din Channels a ranar 4 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Hanya 1 tak da gwamnatin tarayya ta dauka don karya farashin kayan abinci, Ministan Yada Labarai

Labaran NYSC a yau
A halin yanzu matasa 'yan bautar kasa na karbar naira 33,000 a matsayin alawus. Hoto: NurPhoto
Asali: Getty Images

Saboda hauhawar farashin kayayyakin abinci da tsadar rayuwa, masu yi wa kasa hidima na NYSC sun roki gwamnati ta kara musu alawus da ake basu duk wata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da aka tambaye ta ko akwai wani shiri da gwamnatin Tinubu ta yi na kara alawus din, ministar ta amsa da cewa:

“Ba za mu iya ba da tabba tabbaci akan hakan ba. Dukkanmu mun fahimci cewa kudaden shigar gwamnati sun ragu, amma za mu nemo sabbin hanyoyin da za a tabbatar da jin dadin matasan."

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa a halin yanzu matasa masu yiwa kasa hidima na karbar naira 33,000 a matsayin alawus, ci gaban da aka samu a watan Janairun 2020.

Makasudin shirin na NYSC shi ne a koya wa matasan Najeriya muhimmancin sadaukar da kai ga yi wa al’umma aiki.

Kara karanta wannan

Babban labari: CBN ya dakatar da ba gwamnatin tarayya bashi saboda dalili 1 tak

Haka kuma shirin zai jaddada muhimmancin hadin kai da ‘yan uwantakar ‘yan kasa ba tare da la’akari da al’ada ko zamantakewa ba.

Yan bautar kasa na cikin mawuyacin hali

Ko da Legit Hausa ta tuntubi wasu daga cikin matasa masu yi wa ƙasa hidima kan wannan batu na karin alawus, Ibrahim Hamisu ya ce lallai akwai buƙatar ayi hakan.

Hamisu ya ce naira dubu 33 da ake ba matasan yanzu ba kai su mako daya, la'akari da yadda kayan abinci suka yi tsada, sannan zirga-zirgar da suke yi ta zuwa wajen aiki na cin kudi.

"Idan ka yi sa a ka samu dakin kwana a inda aka tura ka yin aiki, to za ka ji da sayen abinci ne kawai, amma idan ba ka samu ba, ka ga dole ne ka rinka biyan kudin abun hawa kullum."

A cewar Ibrahim Hamisu.

Ita kuwa Mufidat Muhammad, cewa ta yi:

Kara karanta wannan

Babban Labari: Tinubu ya bada umarnin fito da metric tan 102, 000 na masara da shinkafa

"Idan har kana son ka tsira da mutuncin ka, musamman idan ke macece, to sai dai a rinka tura maki kudi daga gida, domin naira dubu 33 ba inda take zuwa.
"Kaga ni yanzu, daga gidan da aka bamu zuwa inda nake aiki nakan kashe naira 600 kullum, sannan dole in ci abinci idan na je, ga kuma bukatun rayuwa."

Matasan sun roki gwamnatin da ta kafa wani kwamiti da zai duba yiwuwar karawa 'yan bautar kasar alawus kamar yadda aka kafa na mafi ƙarancin albashi.

Hukumar NYSC ta tura matasa 10 zuwa Indiya

A wani labarin kuma, hukumar gudanarwar matasa masu yi wa kasa hidima (NYSC) ta tura wasu matasa 10 zuwa kasar Indiya domin halartar wani taro na matasa da kungiyar Kadet Corps ta Indiya ta shirya.

An ruwaito cewa ana gudanar da taron ne a kowace shekara don tunawa da zagayowar ranar samun 'yancin kai na kasar Indiya, inda ake samun mahalarta daga Turai, Asiya da Afirka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.