Masana sun bayyana ainihin dalilin tsadar rayuwa a Najeriya

Masana sun bayyana ainihin dalilin tsadar rayuwa a Najeriya

-Akwai dalilai da dama da suka haddasa tsadar rayuwa a Najeriya kama daga faduwar farashin man fetur zuwa tashin goron zabin farashin dalar Amurka har zuwa tsada ko karancin abinci.

-A daidai lokacin da talakawa da al'ummar Najeriya ke fama da hawa-hawar farashin kayayyaki da tsadar abinci da kayan masarufi wasu kwararru akan harkokin tattalin arziki sun fara tsokaci.

Masana sun bayyana ainihin dalilin tsadar rayuwa a Najeriya
Masana sun bayyana ainihin dalilin tsadar rayuwa a Najeriya

Kwararrun na ganin akwai dangantaka tsakanin darajar kudin Nera da na kasashen waje da kuma irin matakai da tsare-tsaren Babban Bankin Najeriya ko CBN yake dauka domin gyara tattalin arzikin kasar da yanzu ya durkushe tun lokacin da Shugaba Muhammad Buhari ya karbi ragamar mulkin kasar.

Dr. Obadiah Mailafiya tsohon mataimakin gwamnan Babban Bankin Najeriya yace matakin da bankin ya dauka akan farashin dala ya kawo rudani kuma ya bude hanyar yin cuwa-cuwa a kasuwar dala da nera. Bankin ya kirkiro farashi wajen hudu maimakon daya lamarin da ya sa aka samu rudani. Wannan shi ya kawo rashin gaskiya.

Abun da kuma yake kawo tsadar rayuwa inji Dr Mailafiya shi ne tsadar abinci. Yawancin abun da al'ummar kasar ke ci daga kasashen waje ake kawosu saboda haka tunda dala tana da tsada dole ne farashin ire-iren abincin da ake shigo dasu su tashi.

Yawan tashin hankalin da ake samu tsakanin manoma da makiyaya, inji Mailafiya su ma sun shafi tsadar rayuwa.

Shi ma Malam Ahmed Yusuf tsohon babban daraktan bankin Unity yace lokaci yayi da Najeriya zata tashi ta ciyar da kanta, ko ta daina ko ta rage dogaro ga kayan waje domin rayuwa ta inganta kuma darajar Nera ta dawo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel