Ana Iya Tura Masu Yi Wa Ƙasa Hidima Filin Daga Suyi Yaƙi, Shugaban NYSC

Ana Iya Tura Masu Yi Wa Ƙasa Hidima Filin Daga Suyi Yaƙi, Shugaban NYSC

- Shugaban hukumar NYSC na kasa, Shuaibu Ibrahim ya ce masu yi wa kasar suna cikin jami'an tsaron Nigeria

- Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim ya ce yan NYSC tamkar sojoji suke kuma ana iya basu horaswa na zuwa yaki idan bukatar hakan ta taso

- Shugaban na NYSC ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa game da kiraye-kiraye da wasu ke yi na cewa a soke shirin na NYSC

Shugaban hukumar NYSC na masu yan yi wa kasa hidima, Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim ya ce masu yi wa kasa hidimar suna cikin jami'an tsaron Nigeria kuma ana iya basu horon zuwa yaki idan bukatar hakan ta taso, The Punch ta ruwaito.

The Nation ta ruwaito cewa Ibrahim ya yi wannan furucin ne yayin tattaunawa da aka yi da shi a ranar Laraba yayin da ya ke magana kan batun kiraye-kirayen da wasu ke yi na cewa a soke tsarin yi wa kasa hidimar.

Ana Iya Tura 'Yan NYSC Zuwa Filin Daga Suyi Yaƙi, Shugaban NYSC
Ana Iya Tura 'Yan NYSC Zuwa Filin Daga Suyi Yaƙi, Shugaban NYSC. Hoto: @MobilePunch
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Hotunan Muggan Makaman Da Ƴan Sanda Suka Ƙwato Daga Hannun Masu Garkuwa Da Ƴan Bindiga

Ya bayyana cewa irin horaswar da aka bawa masu yi wa kasa hidimar na makonni uku na shirya su tamkar sojoji.

Shugaban na NYSC ya ce, "Masu yi wa kasa hidima suna zaman ko ta kwana ne. Suna cikin jami'an tsaro a tsarin kasar nan. Don haka, idan akwai yaki mai tsanani, yan NYSC dinmu masu ilimi ne, sun karantu don haka za a iya horas da su. Za ka ga irin horaswar da ake basu da sauransu.

"Ka duba yadda ake basu horaswa cikin makonni uku kacal a sansanin masu yi wa kasa hidima. Kamar sojoji suke. Za ka ga mai yi wa kasa hidima mace na busa algaitar sojoji, tana buga ganga."

KU KARANTA: Da Ɗuminsa: Soja Ya Bindige Jami'an Kwastam Har Lahira a Seme Border

Ibrahim ya ce a yanzu ne NYSC ke da muhimmanci sosai duba da cewa akwai wasu da ke son ballewa daga kasar.

Ana wajabta yi wa kasa hidimar ga dukkan wanda ya kammala digiri ko HND kuma bai haura shekaru 30 da haihuwa ba a Nigeria muddin ba shi da wata matsala na musamman.

Legit ta zanta da matasa masu bautan kasa biyu don jin ra'ayinsu kan abinda shugaban hukumar yayi.

Firdaws Ishaq, yar bautar kasa dake Kaduna ta bayyana cewa ko kadan ba zata yarda a tura da faggen yaki ba.

"Ko a sansanin horo fareti wahala ne ga wasunmu, ballanta faggen fama. Wannan ba zai yiwu ba," tace.

Rabiu Hassan, wanda ke bautar kasa a Abuja ya bayyana cewa idan za'a basu horon da ya kamata da kuma makamai, babu matsala za'a yi turasu faggen fama.

"Abu ne mai kyau, idan za'a iya basu horo irin na Sojoji na zamani daidai da irin wanda ake baiwa yan ta'adda suke zuwa suke zuwa yakan al'umma. Ba damuwa a hada su (yanbautan kasa) da Sojoji wajen yin aiki tare, " yace

"Ya kamata a basu bindigu na zamani ba irin wadanda ake amfani yanzu ba."

A wani labarin daban, Hukumar Yaki Da Hana Safarar Miyagun Kwayoyi na Kasa, NDLEA, ta ce ta kama wasu mutane da ake zargi da safararmiyagun kwayoyi a birnin tarayya Abuja, The Cable ta ruwaito.

Femi Babafemi, kakakin NDLEA, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi ya ce an kama su ne sakamakon samamen da hukumar ta yi cikin wannan makon.

Cikin wanda aka kama akwai wata Ese Patrick da ake zargi na siyar da miyagun kwayoyi a dandalin Instagram.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel