Kitimurmura: Akwai Yiwuwar Kwankwaso da Abba Su Koma APC, Zaben Intanet Ya Nuna Alama

Kitimurmura: Akwai Yiwuwar Kwankwaso da Abba Su Koma APC, Zaben Intanet Ya Nuna Alama

  • Wani dan Najeriya, Oseni Rufai ya gwada wani zabe a kafar yanar gizo a kan Kano, jihar da ta fi kowacce daukar hankali a Arewacin Najeriya
  • Sakamakon zaben ya nuna cewa, akwai yiwuwar dan gaban goshin Kwankwaso, Abba Kabir Yusuf ya bar NNPP ya koma APC
  • Tuni iskar siyasar jihar Kano ta sauya, inda hankalin jama’a gaba daya ya koma tsagin Kwankwaso da wadanda yake goyon baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan (Copy Editor) sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Kano – Wani ma’abocin Twitter ya tsokano magana, inda ya yi gwajin zabe kan yiwuwar Abba Kabir Yusuf ya koma jam’iyyar APC daga NNPP.

A cewar sakamakon zaben da Oseini Rufai ya yi, akwai kamshin dan gaban goshin Kwankwaso, Abba Gida-Gida ya sako jar hula tare da kama tsintsiyar APC.

Kara karanta wannan

Aikin gama ya gama: Dan takarar PDP ya sha kaye a zaben cike gurbi a Yobe, an fadi wanda ya lashe

Kwankwaso da Abba zai iya komawa APC, hasashen 'yan Twitter
Hasashen 'yan Twitter ya ce akwai yiwuwar Kwankwaso da Abba su koma APC | Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

Legit ta tattaro cewa, an tura sakon gayyata ga ‘yan jam’iyyar NNPP, ciki har da Kwankwaso da Abba kan su koma jam’iyyar APC ta su Ganduje.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wutar da ke ci tsakanin APC da NNPP a Kano

Wannan lamari dai na ci gaba da daukar hankali, domin ‘yan Kwankwasiyya da ‘yan tsagin Ganduje na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu.

Idan baku manta ba, ba a ga maciji tsakanin Ganduje da Kwankwaso, wanda a baya suka kasance a inuwa suke cin kasuwar siyasa tare.

Kwankwaso dai a baya shi ne mai gidan Ganduje, inda a baya ya yiwa Kwankwaso mataimakin gwamnan Kano.

Rikicin me ya hada Ganduje da Kwankwaso?

‘Yar tsama ce da son ran siyasa ya shiga tsakani, wanda tuni ya sa suka raba gari da hanyar tafiya, kowa ya ja zugarsa ta magoya baya.

Kara karanta wannan

Sule Lamido ya fadi abu 1 tak da zai iya fitar da 'yan Najeriya daga kangin da suke ciki

A bangaren kwarya-kwaryar zaben Oseini, an ce akwai 57.5% na yiwuwar Abba da Kwankwaso su hade da Ganduje a APC.

Sai kuma 42.5% da ke nuna yiwuwar su zauna a jam’iyyar NNPP mai kayan marmari da ke mulkin Kano a yanzu.

Ga dai sakamakon zaben:

Kadan daga wainar da ake toyawa a siyasar Kano:

El-Rufai ya fi Kwankwaso farin jini, dan Twitter

A bangare guda, dan soshiyal midiya ya fadi tasirin siyasar Kwankwaso da ElRufai a siyasar Najeriya.

A kalaman da ya yi, ya ce ElRufai ya fi Kwankwaso sanuwa da karbuwa a idon 'yan Najeriya duba da wasu dalilai.

Jama'a a kafar Twitter sun yi ca, inda suka bayyana ra'ayoyinsu game da maganar da matashin dan siyasa ya yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.