Shugaban Kasa a 2027: “El-Rufai Ya Fi Kwankwaso Tarin Magoya Baya”, 'Yan Najeriya Sun Yi Muhawara

Shugaban Kasa a 2027: “El-Rufai Ya Fi Kwankwaso Tarin Magoya Baya”, 'Yan Najeriya Sun Yi Muhawara

  • Wani mai amfani da soshiyal midiya, @A_Y_Rafindadi, ya bayyana wani abu mai ban mamaki da ya gano a baya-bayan nan
  • @A_Y_Rafindadi ya ce abun da ya gano ya kasance a kan manyan yan siyasar arewa kuma tsoffin gwamnoni, Nasir El-Rufai da Rabiu Musa Kwankwaso
  • Legit Hausa ta rahoto cewa mai amfani da dandalin na soshiyal midiya ya yi ikirarin cewa El-Rufai ya fi Kwankwaso magoya baya a kujerar shugabancin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Kaduna, jihar Kaduna - Wani mai amfani da dandalin soshiyal midiya, @A_Y_Rafindadi, ya haifar da zazzafan muhawara a soshiyal midiya da hasashensa kan Nasir El-Rufai da Rabiu Musa Kankwaso.

Matashin ya bayyana cewa tsohon gwamnan na jihar Kaduna, El-Rufai ya fi tsohon gwamnan Kano, Kwankwaso, jagoran 'yan Kwankwasiyya farin jini a kujerar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Babbar Kotu ta dakatar da shugaban APC na jihar arewa daga muƙaminsa, ta faɗi dalili

'yan Najeriya sun yi muhawara kan farin jinin Kwankwaso da El-Rufai
Shugaban Kasa a 2027: “El-Rufai Ya Fi Kwankwaso Tarin Magoya Baya”, Yan Najeriya Sun Yi Muhawara Hoto: Pius Utomi Ekpei, Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

@A_Y_Rafindadi ya yi wani zabe kwanan nan a shafin X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) wanda ya nuna yadda El-Rufai ya doke Kwankwaso.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan rubutun da @A_Y_Rafindadi ya wallafa wanda ya ja hankali sosai, masu amfani da soshiyal midiya da dama sun bayyana ra'ayoyinsu yayin da 'yan Najeriya suke jiran zuwan zaben shugaban kasa a 2027.

Jama'a sun yi martani

Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin martanin jama'a a kasa:

Abdullahi Saulawa ya rubuta:

"Tabbas Nasiru zai yi nasara a kafafen sada zumunta, amma idan aka zo batun talakawa Kwankwaso zai doke shi.
"Ku sa a ranku ni ba na cikin tafiyar Kwankwasiyya amma na san Kwankwaso ya fi hulda da talakawa. Shi ba cikakken 'dan jari hujja ba ne."

Barambu Abdulsalam Umar ya ce:

"Kada ka yaudari kanka kamar 'yan Obidients."

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Jam'iyyar APC ta yi magana kan tsohon gwamnan arewa da ke son tsige Ganduje

Chijioke Godwin ya rubuta:

"Shaharar El-Rufai ya karade ko'ina na Arewa da Kudu, amma da alama Kwankwaso ya shahara ne a iya Kano."

@hallirupaki1 ya ce:

"Elrufa'i mutum ne mai magana daya, duk yadda mutane suka kai ga tunanin aiwatar da abu ba mai yiwuwa bane idan Mallam ya fadi akasin haka, ku yarda da ni sai ya aiwatar, koda kuwa zai rage shi kadai."

Kotu ta bada belin Danbilki

A wani labarin kuma, mun ji cewa kotun Majistare da ke Kano ta ba da beli ga fitaccen dan siyasa, Abdulmajid Danbilki Kwamanda kan kudi miliyan daya.

Jigon APC, Kwamanda an cafke shi ne a ranar 23 ga watan Janairu kan zargin neman ta da fitina inda aka tsare shi a gidan gyaran kaso.

Asali: Legit.ng

Online view pixel