An Gano Gawar 'Yar Jami'ar Najeriya a Dakin Kwananta

An Gano Gawar 'Yar Jami'ar Najeriya a Dakin Kwananta

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Jihar Ondo - An gano gawar daliban jami'ar Adekunle Ajasin, Akungba (AAUA) a dakinta a karshen wannan makon.

Marigayiyar, wacce aka gano sunanta a Ifeoluwa Adekunle, yar aji 300 a tsangayar nazarin tattalin arziki wato 'Economics'.

An tsinci gawar dalibar jami'ar Najeriya a dakinta
'Yan sanda sun fara bincike bayan gano gawar dalibar jami'a a Ondo. Hoto: Rundunar 'Yan Sandan Najeriya
Asali: Twitter

An tattaro cewa dalibar, maharan sun kai wa dalibar wacce ke zaune a wajen harabar makaranta lokacin ita kadai ne a dakinta, rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kisan dalibar ya tayar da hankulan mu

Wani majiya, wacce ya nemi a boye sunanta, ya ce kisar ya tada hankulan sauran dalibai, tana mai cewa tuni an kai wa 'yan sanda rahoton abin da ya faru.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Katsina ta dauki gagarumin mataki bayan 'yan bindiga sun kwashe 'yan kai amarya 60

Ya ce:

"Mun tsince ta kwance cikin jini a dakinta. Wasu da har yanzu ba a tantance ko su waye ba da suka zo ziyara sun caka mata wuka ta mutu. Mun san ba aikin kungiyar 'yan asiri bane kamar yadda wasu mutanen ke cewa."
"Mun kai wa 'yan sanda rahoton kisan amma kamar ba suna jan jiki wurin gano wadanda suka aikata wannan mummuna laifin.
"Muna kira ga gwamnatin jihar Ondo ta taimaka ta duba lamarin su tabbatar an yi wa wacce aka kashe adalci."

'Yan sanda sun fara bincike don gano wanda ya yi kisan

Da ta ke tabbatar da lamarin cikin hira da aka yi da ita ranar Lahadi, Kakakin 'yan sandan jihar Ondo, Funmilayo Odunlami-Omisanya, ya ce ana bincike.

Odunlami-Omisanya ya ce an kai gawar wacce abin ya faru da ita dakin ajiye gawa na asibiti.

Ta ce:

"An kashe ta amma an kai gawarta asibiti kuma mun fara bincike.

Kara karanta wannan

‘Yan sanda sun kama wasu gungun mutanen da ake zargi da sace akwatunan zabe a Kano

"Ba mu tabbatar ko aikin 'yan kungiyar asiri bane amma an kashe ta a dakinta da ke wajen makaranta amma binciken mu zai bayyana abin da ya yi sanadi."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164