FAAN: Ministan Tinubu Ya Bayyana Alfanun da Za a Samu Kan Mayar da Ofishin Legas, Ya Fadi Dalili
- Festus Keyamo ya bayyana yawan makudan kudade da Gwamnatin Tarayya za ta samu kan mayar da FAAN Legas
- Keyamo ya ce akalla mayar da ofishin zai rage musu yawan kashe kudade har naira miliyan 943 a Najeriya
- Wannan na zuwa ne yayin da ake ta cece-kuce kan mayar da ofishin FAAN Legas daga birnin Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Ministan Harkokin Jiragen Sama a Najeriya, Festus Keyamo ya bayyana alfanun mayar da ofishin FAAN jihar Legas.
Keyamo ya ce akalla mayar da ofishin zai rage musu yawan kashe kudade har naira miliyan 943 a Najeriya.
Mene Keyamo ke cewa kan FAAN?
Ministan ya bayyana haka a yau Juma'a 2 ga watan Faburairu yayin wata ganawa da ma'aikatansa a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mista Festus ya koka kan yadda Gwamnatin Tarayya ta ke kashe kusan naira biliyan 1 kan ma'aikatan FAAN daga Abuja zuwa Legas, cewar Tribune.
Ya ce:
“Ina da tabbacin kun saurari hira ta a kwanakin nan inda na fayyace komai, ina fatan 'yan uwa na daga bangaren kasar za su fahimci abin."
Yawan kudaden da aka samu rara
Ya kara da cewa:
"Kawai ina ganin ba su fahimci abin da muke shirin yi a baya, na nemi lissafin inda na tuntubi ma'aikatan su ba mu.
"Yawan alawus na tafiye-tafiye kadai muna biyan kudade ya kai naira miliyan 493 a 2023 kadai da kuma tikiti naira miliyan 450.
Keyamo ya ce dukkan wannan kudaden an kashe su ne saboda rashin kasancewar masu ruwa da tsakin hukumar a wuri daya, cewar Vanguard.
Minista ya fadi amfanin cire tallafi
Kun ji cewa Ministan yada labarai, Mohammed Idris ya bayyana amfanin cire tallafin mai a Najeriya.
Idris ya ce tabbas cire tallafin ya taimaki kasar wurin yin amfani da kudaden don yin ayyukan ci gaban kasar baki daya.
Ya ce cire tallafin alkairi ne saboda idan da ba a cire ba da mawuyacin halin da za a shiga har sai yafi wanda ake ciki yanzu.
Asali: Legit.ng