Ma’aikatan Tarayya Sun Fara Nunawa Gwamnati Yatsa, Ba Su Samu Albashin Watan Janairu Ba

Ma’aikatan Tarayya Sun Fara Nunawa Gwamnati Yatsa, Ba Su Samu Albashin Watan Janairu Ba

  • Sakamakon rashin samun albashin watan Janairu, ma'aikatan tarayya sun fara nunawa gwamnati yatsa da 'yan guna-guni
  • An ruwaito cewa laifin na daga ofishin akanta janar na kasa, wanda kuma ya yi alkawarin sakarwa ma'aikatan albashin su a jiya Alhamis
  • Gaza samun albashin a jiya tilasta wasu ma'aikatan fara 'yan kananun maganganu, inda Legit Hausa ta ji ta bakin wani ma'aikaci

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Ma'aikatan tarayya sun fara 'yan guna-guni yayin da gwamnati ta gaza cika alkawarin da ta dauka na yin albashi a ranar Alhamis.

Ba iya batun biyan albashin ne ke damun ma'aikatan ba, har da batun naira dubu 35 da aka yi masu alkawarin kari kan albashin nasu.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya yi magana mai zafi bayan fashewar wani abu ta yi ajalin rayukan bayin Allah

Gwamnatin tarayya ba ta biya albashin ma'aikata na Janairu ba.
Gwamnatin tarayya ba ta biya albashin ma'aikata na Janairu ba. Hoto: @Modrismalagi
Asali: Twitter

Kungiyar NCSU ta fara korafin rashin albashi

The Guardian ta ruwaito cewa ofishin akanta janar na kasa, OAGF, ne ya gaza kammala aiki a manhajar kudaden tarayya (GIFMIS) na 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gaza kammala aikin ya kawo tsaiko wajen biyan ma'aikatan tarayya albashin watan Janairu, kamar yadda sakataren kungiyar NCSU ya sanar.

Sakataren kungiyar ma'aikatan gwamnati a Najeriya, Bomoi Mukammed Ibraheem ya shaidawa jaridar Vanguard cewa ba a biya albashi ba har yanzu.

Abin da ma'aikata ke cewa

Wani ma'aikaci a sakatariyar tarayya da ke Abuja, ya ce:

"Ran ma'aikatan tarayya ya baci saboda tsaikon biyan albashin. Kowa ya san halin da ake ciki a Najeriya.
"A watan Satumba ne kawai aka biya naira dubu 35 ta janye tallafin man fetur da aka yi wa ma'aikatan alkawari, don haka dole mu nuna yatsa."

Kara karanta wannan

FAAN: Ministan Tinubu ya bayyana alfanun da za a samu kan mayar da ofishin Legas, ya fadi dalili

Domin kwantar da hankulan ma'aikatan ta, tuni hukumar cibiyar darasin lissafi ta Najeriya ta sanar da ma'aikata cewa kar su tsammaci samun albashi don nan kusa.

Ma'aikata sun koma kamar almajirai - Ahmad

Wani da Salahu Ahmad (ba asalin suna ba) da ya zanta da Legit Hausa ya nuna matukar damuwarsa kan yadda har zuwa ranar Juma'a ba su samu albashi ba.

Mallam Ahmad ya ce tun kusan ranar 20 ga watan Janairu kayan abinci a gidansa suka kare, har zuwa wannan rana yana karbar bashin kudi ne da zummar biya idan aka yi albashi.

A cewarsa:

"Watakan Mallam, rayuwar nan kawai sai dai mu yi addu'a, amma aikin gwamnati ya koma kamar almajiri mai rokon abinci daga hannun masu arziki.
"A kudin mota daga gidana zuwa aiki nakan kashe naira dubu 20 kowanne wata, sannan ina cin abinci a wajen aiki, yakan yi wahala wata ya zo ya wuce ban ci bashin kudi ba."

Kara karanta wannan

An ci tarar wani kamfanin Amurka dala 70,000 saboda ya tilasta ma'aikaci Musulmi ya aske gemu

Mallam Ahmad wanda ma'aikacin gwamnatin tarayya ne ya koka kan yadda ba a cika biyan alawus na aiki, ko biyan kudin wata 13 a shekara ba.

Ya ce akwai bukatar gwamantin tarayya ta fifita walwalar ma'aikata, saboda sai da su ne shugabancin kasar ke tafiya.

Gwamnati ta ba 'yan Najeriya hakuri kan matsin rayuwa

A wani labarin, gwamnatin tarayya ta roki 'yan Najeriya su kara hakuri da matsin rayuwar da suke fuskanta, tana mai cewa Shugaba Tinubu na sane da komai.

Ministan yada labarai, Mohammed Idris Malagi ya yi rokon yayin da ya ke tabbatar wa 'yan Najeriya cewa suna dab da fara shan romon kudurorin da Tinubu ke aiwatarwa.

Mista Malagi ya ce Tinubu na yin iya bakin kokarin sa don dawo da martabar Najeriya a idon duniya, kuma sauye-sauyen na iya shafar tattalin arziki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel