Rikita-rikita Yayin da Tsohon Akanta-janar Ya Tona Asirin EFCC Kan Yarjejeniyarsu, Ya Fadi Dalilai

Rikita-rikita Yayin da Tsohon Akanta-janar Ya Tona Asirin EFCC Kan Yarjejeniyarsu, Ya Fadi Dalilai

  • Yayin da ake ci gaba da shari'ar tsohon Akanta-janar, Ahmed Idris ya tona yadda hukumar EFCC ta yaudare shi
  • Ana zargin Idris da badakalar makudan kudade har naira biliyan 109.4 wanda aka kama tun watan Mayun 2022
  • Ahmed Idris ya ce hukumar ta yaudare shi inda ya amince akwai hannunsa a cikin badakalar tare da masa alkawari

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon Akanta-janar ya bayyana yadda hukumar EFCC ta yaudare shi ya amince da badakalar naira biliyan 109.4.

Ahmed Idris ya ce hukumar ce ta yaudare shi inda ya amince akwai hannunsa a cikin badakalar, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Mai ba Jonathan shawara ya nunawa Tinubu hanyar farfado darajar Naira kan Dala

Tsohon Atoni-janar ya fadi ydd ta yaudare shi
Tsohon Akanta Janar ya yi dana sanin amincewa da bukatar EFCC. Hoto: Ahmed Idris, EFCC Nigeria.
Asali: Facebook

Mene ake zargin Idris a kai?

An kama Idris ne a ranar 16 ga watan Mayun 2022 kan zargin badakalar makudan kudade da wasu mutane.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran wadanda ake zargin sun hada da Geoffrey Akindele da Mohammed Kudu Usman da wani kamfani, Gezawa Commodity Market and Exchange Limited.

Mai Shari'a, Halilu Yusuf ya umarci bincike kan bayanan tsohon Akantan ga hukumar EFCC don tantance su.

Kotun ta dauki matakin ne ko za ta iya daukar bayanan da kum saka su a jerin shaidun da ta ke da shi, Vanguard ta tattaro.

Yaudarar da EFCC ta yi kan shari'ar

Lauyan wanda ake zargi, Chris Uche ya ce EFCC ta fada wa Ahmed cewa ba za ta ci gaba da shari'arsa ba idan ya ba da bayanai da za su zurma tsohuwar Ministan kudade da wasu gwamnoni.

Kara karanta wannan

Duk da suka daga 'yan Arewa ministan Tinubu ya dage kan mayar da FAAN zuwa Legas, ya fadi dalili

Idris ya bukaci kotun ta yi watsi da bayanan nasa inda ya ce hakan ya sabawa doka don ya yi su ne ba a gaban lauyoyinsa ba.

Har ila yau, hukumar EFCC ta bakin wani daga cikin lauyoyita, Hayatudden Sulaiman ya yi fatali da zargin.

Daga bisani kotun ta dage ci gaba da sauraran shari'ar har sai ranar 20 ga watan Maris mai zuwa.

Kotu ta ba da belin Danbilki Kwamanda

Kun ji cewa kotun Majistare a Kano ta ba da belin jigon APC, Abdulmajid Danbilki Kwamanda.

Kotun ta ba da belin ne kan kudi har naira miliyan daya da kuma masu tsaya masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.