An Shiga Tashin Hankali Bayan 'Yan Bindiga Sun Guntule Kan Sifetan Dan Sanda, Bayanai Sun Fito

An Shiga Tashin Hankali Bayan 'Yan Bindiga Sun Guntule Kan Sifetan Dan Sanda, Bayanai Sun Fito

  • An shiga tashin hankali bayan 'yan bindiga sun guntule kan sifetan dan sanda a birnin Uyo da ke jihar Akwa Ibom
  • Rahotanni sun bayyana marigayin da suna Osang inda maharan suka kai masa farmaki a yankin Afaha Ube da ke Uyo
  • Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Odiko Mac ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Alhamis 1 ga watan Faburairu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Akwa Ibom - An shiga tashin hankali a jihar Akwa Ibom bayan 'yan bindiga sun guntule kan wani sifetan dan sanda.

Lamarin ya faru ne a daren jiya Laraba 31 ga watan Janairu yayin da 'yan bindigan suka far masa.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Yan bindiga sun farmaki manyan sarakunan gargajiya 3 tare da ajalin 2, bayanai sun fito

Sifetan dan sanda ya gamu da ajalinsa a hannun 'yan bindiga
Mahara sun hallaka sifetan san sanda a Akwa Ibom. Hoto: NPF.
Asali: Twitter

Yaushe aka hallaka dan sandan?

The Nation ta tattaro cewa an bayyana marigayin da suna Osang inda maharan guda kai 10 suka kai masa farmaki a yankin Afaha Ube da ke Uyo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu shaidun ganin da ido sun tabbatar da cewa maharan sun yi ta harbin bindiga kafin suka aikata ta'asar.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Odiko Mac ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Alhamis 1 ga watan Faburairu.

Martanin 'yan sanda kan lamarin

Odiko ya bayyana lamarin da abin takaici inda ya ce rundunar ta samu labarin mummunan lamarin, cewar Vanguard.

Ya ce:

"Mun samu mummunan labarin kuma abin takaici ne.
"Tuni aka fara gudanar da bincike kuma an baza jami'an tsaro lunguna da sako don zakulo waɗanda suka aikata laifin.
"Ba za mu gajiya ba za mu ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da kuma ganin masu aikata laifuka sun girbi abin da suka shuka.

Kara karanta wannan

Labari Mai Dadi: Shugaban jam'iyyar PDP a jihar Legas ya shaki iskar 'yanci

Har ila yau, Gwamnan Umo Eno ya gargadi masu aikata laifuka da su guji fushin gwamnatinsa inda ya ce ba za su ji ta dadi ba.

'Yan bindiga sun hallaka sarakunan gargajiya 2 a Ekiti

A wani labarin, Wasu 'yan bindiga sun hallaka masu rike da sarautar gargajiya har guda biyu a jihar Ekiti.

Lamarin ya faru ne a ranar Talata 30 ga watan Janairu yayin da suke dawowa daga ganawar tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel