NCC Za Ta Hana Masu Layin GLO Kiran MTN Kan Wani Babban Dalili 1, Ta Tura Gargadi

NCC Za Ta Hana Masu Layin GLO Kiran MTN Kan Wani Babban Dalili 1, Ta Tura Gargadi

  • Masu amfani da layin GLO za su fuskanci matsala bayan hukumar NCC ta kakaba doka ga kamfanin kan kiran layin MTN
  • Hukumar ta ce dokar za ta shafi masu layukan GLO da ke mu'amala da masu layukan MTN kan rashin biyan wasu kudaden da GLO ya yi
  • Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran hukumar, Reuben Mouka ya fita a yau Litinin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Hukumar Sadarwa a Najeriya (NCC) ta sanar da cewa za ta dakatar da masu amfani da GLO kiran layukan MTN.

Hukumar ta ce ta dauki wannan matakin ne saboda basukan da ke tsakanin kamfanonin biyu kan kudin kira, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Binciken N37bn: An wuce wurin, Hukumar EFCC ta dauki mataki kan ministar Buhari, ta fadi dalili

NCC za ta dauki mataki kan masu amfani da GLO saboda basuka
Hukumar NCC za ta hana masu MTN kiran layukan GLO. Hoto: NCC.
Asali: UGC

Mene ake zargin GLO da aikata wa MTN?

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran hukumar, Reuben Mouka ya fitar a yau Litinin 8 ga watan Janairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce GLO ta samu takardar korafi daga kamfanin MTN inda ta ba ta damar yin martani a kai, Newstral ta tattaro.

A cewar sanarwar:

"An bayyana wa Kamfanin GLO korafin da MTN ya shigar inda aka ba shi damar yin martani.
"Hukumar bayan ta yi nazari mai zurfi, ta fahimci cewa GLO ba shi da wani uzuri na rashin biyan basukan."

Lokuta da dama hakan ya faru tsakanin GLO da MTN

Hukumar ta ce nan da kwanaki 10 da wa'adin zai kare, masu GLO ba za su samu damar kiran MTN ba.

Ta ce dakatar da kiran har ila yau, zai ba da damar kiran layukan Glo din na tsawon wannan lokaci.

Kara karanta wannan

Jerin manyan mata yan siyasa 7 da aka zarga da cin hanci a Najeriya

Wannan ba shi ne karon farko da ake haramta wa masu amfani da layukan GLO kiran masu MTN ba kan matsala guda daya.

A shekarar 2019, MTN bayan samun umarni daga Hukumar NCC ta dakatar da kiran layukansu daga GLO saboda basukan naira biliyan hudu.

Za a kara kudin Data da katin waya

A wani labarin, Kamfanonin sadarwa sun bukaci a ba su dama su kara kudin Data da kiran waya a Najeriya.

Masu hawa internet za su sake shiga tasku ganin yadda yanzu ma ake kuka kan yadda kamfanonin ke zukar data da katin waya.

Tun a watan Nuwamban shekarar da ta gabata, kamfanonin sadarwa suka roki gwamnati da ta amince da bukatarsu ta sake yin bitar farashin kudaden.

Asali: Legit.ng

Online view pixel