Rikicin makiyaya da manoma: Sojojin saman Najeriya za su tare a jihar Taraba
- Sojojin saman Najeriya za su tare a jihar Taraba
- Shugaban rundunar sojin saman Najeriya Sadique Abubakar ya sanar da hakan a jiya
- Za'a kafa sansanin ko ta kwana a tsakanin jahohin Benue da Nasarawa
Shugaban rundunar sojin saman Najeriya Sadique Abubakar a jiya ya sake nanata kudurin rundunar na kafa wani sansanin aiki a jihar Taraba dake a yankin arewa maso gabashin kasar nan da nufin dakile dukkan rikece-rikicen da yankin ke fama da su.
KU KARANTA: Za'a kawo karshen wahalar mai wannan watan
Safsan sojin dai ya bayyana haka ne a yayin da yake gabatar da wata makala ga sabbin jami'an rundunar da suka kammala daukar horon su a garin Abuja.
Legit.ng ta samu cewa haka zalika Sadique Abubakar ya kuma bayyana cewa rundunar har ila yau za ta kafa sansanin ko ta kwana a tsakanin jahohin Benue da Nasarawa duk dai don tabbatar da tsaro musamman ma yanzu da yankin ke fama da rikice-rikecen manoma da makiyaya.
A wani labarin kuma, Rundunar sojin kasan Najeriya ta sanar da kammala dukkan shire-shiren da suka wajaba wajen tabbatar da gina sabon barikin sojoji a garin Jalingo, babban birnin jihar Taraba domin tabbatar da tsaro.
Babban hafsan sojojin na bataliya ta 3 dake a garin Jos Manjo Janar Benjamin Ahanotu ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar bangirma da ya kaiwa gwamnan jihar ta Taraba Mista Darius Ishaku a ofishin sa.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng