Kamfanin MTN Zai Tattara Komai Nashi Ya Fice Daga Najeriya Saboda Wasu Dalilai

Kamfanin MTN Zai Tattara Komai Nashi Ya Fice Daga Najeriya Saboda Wasu Dalilai

  • Kamfanin sadarwa na MTN ya yi barazanar barin ayyukansa a Najeriya bisa wasu dalilai
  • Kamfanin ya koka kan yawaitar aikata ta'addanci, wanda ke kawo barazana ga ayyukansa
  • Hakazalika ya bayyana cewa, za a samu matsaloli a 'yan kwanakin nan masu zuwa da layin

Kamfanin MTN ya yi gargadin yiwuwar dakatar da ayyukansa a Najeriya sakamakon karuwar matsalar rashin tsaro a sassa daban-daban na kasar, TheCable ta ruwaito.

MTN, a wani sako da kamfanin dillacin labarai na Reuters ya gani, ya sanar da kwastomominsa game da yiwuwar jinkiri a hulda dashi.

“Abin takaici, dole ne mu sanar da ku cewa tare da karuwar rashin tsaro a sassa daban-daban na Najeriya; zaku iya samun tseko a sabis dinmu a cikin kwanaki masu zuwa,” kamar yadda aka ruwaito MTN ya ce.

KU KARANTA: Babban Hadimin Gwamna Ya Tsallake Rijiya Ta Baya, an Yi Awon Gaba da Shanunsa

Kamfanin sadarwa na MTN ya yi barazanar barin Najeriya saboda wasu dalilai
Ofishin kamfanin sadarwa na MTN | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

"Wannan yana nufin cewa a wasu lokuta, jami'an ba da tallafinmu na fasaha ba za ta iya isa ga yankunanku ba kana su sami lokacin gyara mafi kyau domin kula da matsalolinku cikin gaggawa ba.''

Kamfanin MTN na Najeriya ya zama kamfani na farko da ya amince da yiwuwar dakatar da ayyukansa saboda matsalar rashin tsaro a kasar.

A cewar wani rahoto na SB Morgan (SBM) Intelligence, an kashe daruruwan 'yan Najeriya a cikin wasu munanan hare-hare da suka faru a sassa daban-daban na kasar a watan Afrilu.

A cikin wani rahoton da aka buga kwanan nan ‘Rahoton Bayanan Fasahar Sadarwa’, ta Ofishin Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS), ya ce yawan masu amfani da layukan intanet ya ragu da 6.06% cikin 100% a zangon farko na 2021 (Q1 2021).

Rajistar masu amfani da layuka wajen kira kuma ya sami ragin 5.96% kamar yadda adadin masu amfani ya fadi daga miliyan 204.6 a cikin zango na hudu na 2020 zuwa miliyan 192.4 a cikin zango na farko na 2021.

A halin yanzu, Bayanai daga NBS sun nuna cewa MTN ya fi yawan masu amfani da yanar gizo a Najeriya wanda ya kai kimanin miliyan 61.58, sai kuma kamfanin Glo, Airtel, da 9Mobile da ke da miliyan 38.81, miliyan 37.78, da kuma miliyan 6.42 bi da bi.

KU KARANTA: Ghali Na’Abba Ya Bayyana Yadda Gwamnoni Suka Jefa Najeriya Cikin Matsaloli

A wani labarin, Shugaban Matasan na kasa na jam’iyyar APC, Ismaeel Ahmed, a ranar Laraba, ya ce Gwamnatin Tarayya ba ta hana amfani da Twitter ba, kawai ta dakatar da ayyukan ta ne.

Ya fadi haka ne a wani taron manema labarai da yake gabatarwa wanda aka sake tsarawa domin ci gaban taron matasa wanda zai gudana a mako mai zuwa, Punch ta ruwaito.

Ahmed ya ce: “Gwamnati ba ta hana shafukan sada zumunta ba kamar yadda mutane da yawa za su yi zato.

"Yana da mahimmanci mu sani cewa Facebook har yanzu yana aiki, Instagram har yanzu yana aiki, WhatsApp yana aiki, kuma da yawa sauran dandamali na dandalin sada zumunta duk suna aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel