Ana Daf da Auren Malamin Makarantar Allo, Matsafa Sun Yanke Mazakutarsa a Zaria

Ana Daf da Auren Malamin Makarantar Allo, Matsafa Sun Yanke Mazakutarsa a Zaria

  • Rahoton da muke samu ya bayyana yadda wasu matsafa suka yanke al’aurar wani malamin makarantar allo a Kaduna
  • An yiwa malamin kisan gilla kafin daga bisani aka gano tuni an yanke wani sashe na jikinsa, lamarin da ya tada hankali
  • Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, inda tace a halin yanzu ana ci gaba da bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Soba, jihar Kaduna - Wani rahoto mai daukar hankali ya bayyana yadda wasu matsafa suka yanke mazakutar wani malamin allo a unguwar Awai da ke karamar hukumar Soba ta jihar Kaduna.

An ruwaito cewa, matsafan sun yiwa mutumin mai suna Alaramma Salisu Mai Almajirai yankan rago tare da yi masa aika-aikar yanke mazakutarsa a hanyarsa ta dawowa daga karbo kayan cin angoncinsa.

Kara karanta wannan

An kama 1 daga kasurguman 'yan bindigan da suka sace Nabeeha da 'yan uwanta a Abuja

An yanke mazakutar wani malamin allo a Zaria
Ana yanke mazakutar malamin allo a Zaria ana daf da bikinsa | Hotunan da aka saka na nuna misali ne kawai, ba ainihin abin da ya faru ba kenan
Asali: Getty Images

Rufa’i Waziri, Sarkin Awai ya shaidawa Aminya cewa, mazauna yankin sun shiga tashon hankali a sadda suka tsinci gawar Alaramma a yashe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka gano an yi masa barna a jikinsa

Ya kuma bayyana cewa, sun gano an cire mazakutarsa ne bayan da aka gano gawar kwance a wani wuri a yankin.

Hakazalika, ya ce wannan bawan Allah da aka kashe mutumin kirki ne, kuma ba shi da abokin fada ko hatsaniya a Awai.

Sarkin ya yi addu’ar Allah ya tona asirin wadanda suka yi wannan bakin aiki, inda ya nemi hukumomin tsaro da su yi aikin gano wadanda suka yi kisan gillar.

Matar marigayi ta magantu

Uwar gidansa, Malama Zulaihat ta shaidawa jaridar yadda lamarin ya faru, inda ta ba da labarin har yadda ta tuntubi budurwar da zai aura don sanin inda yake.

Kara karanta wannan

Dan yahoo ya soki mahaifansa saboda sabulun tsaki da zai kawo mas kudi ya ki aiki, laifinsu 1 tak

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandar Jihar Kaduna ASP Mansir Hassan, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace a halin yanzu ana ci gaba da bincike don gano mashekan.

Ana yawan samun rahotannin kisan gilla a bangarori daban-daban na Arewacin Najeriya, hakan ba zai rasa nasaba da rashin tsaro da ke addabar yankin ba.

An kama dan bindiga a Kaduna

A wani labarin, rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar 20 ga watan Janairun 2024 sun kame Muhammad Bello, wani matashi mai shekaru 28 dan asalin Zamfara a jihar Kaduna.

Ana zargin Bello na daya daga masu garkuwa da mutanen da suka addabi al’umma da sace-sace a yankin.

Babban jami’in ofishin yanki na Tafa ya bayyana cewa, an kai ga kame matashin ne bayan samun bayanan sirri, inda aka yi ram dashi a wani otal da ke yankin Tafa a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel