Manyan Masu Kudin Duniya Sun Samu Karayar Arziki, Dangote ne Kadai Ya Samu Riba

Manyan Masu Kudin Duniya Sun Samu Karayar Arziki, Dangote ne Kadai Ya Samu Riba

  • Manyan biloniyoyin duniya da suka shahara a fannin arziki sun shiga wani mawuyacin hali na girgizar arziki a ranar Litinin da ta gabata
  • Bernard Arnault, Elon Musk, Jeff Bezos da Bill Gates sun hango rushewar tattalin arzikinsu da kaso daban-daban wanda Gautam Adani ya fi su asarar dukiya
  • Aliko Dangote, attajirin da yafi kowa kudi a Afirka, ya samu hauhawar dukiya, inda ya samu $8.56 miliyan cikin awanni 24

Ranar Litinin, 30 ga watan Janairu, 2023 ta zama ranar bakin ciki ga manyan attajiran duniya yayin da tattalin arzikinsu ke rushewa a bangarorin fasaha, saiduwa, sari da samarwa.

Attajirai
Manyan Masu Kudin Duniya Sun Samu Karayar Arziki, Dangote ne Kadai Ya Samu Riba. Hoto daga Maurice Greene
Asali: Getty Images

Manyan biloniyoyi tara na duniyan sun hango yadda kafatanin tattalin arzikinsu ke sauka yayin da kayyakinsu suke ta rage karbuwa daga masu narka hannayen jari.

1. Attajirin kasar Faransa da yafi kowa arziki a duniya, Bernard Arnault, ya hango yadda karayar ke masa barazana yayin da tattalin arzikinsa ya sauka daga $190 biliyan zuwa $189 biliyan a cikin awanni 24.

Kara karanta wannan

Fasto Ya Yada Labarin Karya Cewa Ya Mutu Gudun Kada Ya Biya Bashin N3m

2. Mamallakin kamfanin Tesla, Elon Musk, wanda ya hango asara na tunkarosa ya yi asarar $20 biliyan a makon da ya gabata.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hakan ya janyo rushewar kafatanin tattalin arzikinsa da $7 biliyan wanda dukiyarsa ta koma $160 biliyan daga $167 biliyan kamar yadda binciken Juma'a, 27 ga watan Janairu, 2023 ya nuna.

Yayin da kayyakin kamfanin Tesla suke rage saiduwa a kasuw da kashi 3 bisa dari, kayan kashi 11 ne aka siyar a makon da ya gabata.

3.Jeff Bezos, mamallakin kamfanin Amazon, ya yi asarar $1 biliyan na kayyakin kamfanin kasuwancin yanar gizon da yafi kowanne girma.

Sun siyar da kasa da yadda ake sa rai ranar Litinin, 30 ga watan Janairu, 2023.

4. Bill Gates wanda shi ne na hudu a jerin attajiran duniya a kididdigar Bloomberg Billionaire, ya yi asarar kimanin $953 miliyan, hakan ya saukar da arzikinsa zuwa $111 biliyan.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Yan Bindiga Sun Farmaki Ofishin INEC da Caji Ofis, Sun Halaka Mutum 1

5. Biloniyan kasar India, Adani, ya fi kowa tafka asara, wanda shi ne attajirin da ya fi kowa arziki a kasar India da nahiyar Asiya.

Gautam Adani ya yi asarar sama da $65 biliyan a rana daya, wanda hakan ya sawarwaroshi zuwa mataki na 11 a jerin attajiran.

Adani ya rasa matsayinsa na attajirin duniya na uku ga Bezos a makon da ya gabata yayin da ya koma na biyar a jerin.

Amma wani rahoton da Hindenburg, wani kamfanin bincike, ya kara bayyana wata mummunar asara da Adani ya yi na dukiyarsa wanda ya rasa hannayen jari da dama a kamfaninaa. Wannan ne ya yi sanadiyyar saukarsa daga jerin attajiran duniya.

6. Dan Afirka da ya fi kowa arziki, Aliko Dangote, ya samu hauhawar dukiyarsa cikin awanni 24, inda ya samu ribar $8.56 miliyan.

Duk da yadda ya sauka daga mataki 80 zuwa 84, dukiyar Dangote tana nan a $19 biliyan. Wannan na da alaka da yadda masu narka hannun jari suka yi amanna da hannun jarinsu a simintin Dangote, kamfanin simintin da ya fi kowanne girma a Afirka.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Gwamnan CBN ya Dira Majalisar Tarayya, Ya Shiga Ganawa da Kakakin Majalisa

Elon Musk ya tafka asara

A wani labari na daban, Legit.ng ta ruwaito yadda mai kamfanin Tesla, Elon Musk ya yi asarar dukiyarsa da kusan $11 biliyan tun daga lokacin da ya fara fuskantar shari'a kan wallafarsa ta Twitter.

Kididdigar Bloomberg Billionaire ya nuna yadda mai kamfanin SpaceX ya tafka asar $10.6 biliyan wanda ya tsaya a $145.2 biliyan tun daga lokacin da ya fara shari'a a kotu ranar Juma'a, 20 ga watan Janairu, 2023.

Ribar da Musk ya samu ta karshe ita cr tun a watan Nuwamba 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel