Za a kammala titin Abuja-Kaduna-Kano kafin karshen shekarar 2023

Za a kammala titin Abuja-Kaduna-Kano kafin karshen shekarar 2023

- Adebiyi ya bayyana cewa za a kammala titin Abuja-Kaduna-Kano kafin wa'adin wannan gwamnati ya kare inda ya ce an ci karfin aikin

- Ya bayyana haka ne lokacin da ya ke ziyarar duba aiki a Kano tare da tabbatar da cewa sun gamsu da ingancin aikin

- Ya bawa al'umma hakuri kan yanayin aikin tare da shawartar dan kwangila da ya kara dagewa don kammaluwar aikin cikin lokaci

Mista Funso Adebiyi, Shugaban sashin Gini da Gyaran Manyan Tituna, Ma'aikatar Ayyuka da Gidaje, ya ce za a kammala aikin ginin titin Abuja-Kaduna-Kano kafin karshen shekarar 2023.

Adebiyi ne ya bayyana haka lokacin da ya ke duba ci gaban aikin a Kano ranar Juma'a, The Nation ta ruwaito.

Za a kammala titin Abuja-Kaduna-Kano kafin karshen 2023
Za a kammala titin Abuja-Kaduna-Kano kafin karshen 2023. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

"Aikin sake fasalin titin Abuja-Kaduna-Kano wanda ake ta samun cigaba za a kammala shi kafin wa'adin wannan gwamnati ya kare.

"Mun gamsu da ingancin aikin kuma muna kokari muga an kara sauri a aikin.

"Kuna iya ganin yadda aiki ke gudana a duka bangarorin titin mai nisan kilo mita 375 daga Abuja-Kaduna-Kano," a cewar sa.

Daraktan ya bukaci yan Najeriya da su ci gaba da hakuri da gwamnati a kokarin da ta ke na samar da ingantaccen aiki wanda za a dade ana mora.

DUBA WANNAN: NDLEA ta fitar da sunayen wadanda suka yi nasara da za a dauka aiki

Ya kuma roki masu amfani da titi da su ci gaba da hakuri da yanayin titi har zuwa lokacin da za a kammala aikin.

"An samu ci gaba sosai. Saboda an kammala fiye da kilo mita dari duk da ba a jere ba, an kammala bangare na daya zuwa na uku (Abuja - Kano)," a cewar sa.

Ya ce an kammala kilo mita 40 a bangare na biyu (Kaduna-Zaria), da kilo mita 70 karkashin bangare na uku (Zaria-Kano).

"Kuma ana kan kammala bangarori da dama na titin, ana kuma cike guraren da ke da bukatar gyara don saukakawa masu bin titin.

KU KARANTA: Hanan Buhari tare da mijinta Turad sun tafi Dubai don bikin zagayowar ranar haihuwarsa (Bidiyo da Hotuna)

"Yana da kyau in gyara furucin masu cewa aiki baya tafiya.

"Muna aiki tukuru don ganin mun kammala aikin lokacin da aka diba tare da yin ingantaccen aiki", kamar yadda ya bayyana.

Ya kuma bukaci dan kwangilar da ya kara sauri da kuma diban karin ma'aikata don kammaluwar duka bangarorin titin.

A wani labarin daban, rikici ya kaure a zauren majalisar Jihar kasar Ghana a jiya Laraba 6 ga watan Janairu bayan rushe majalisar kunshi ta bakwai.

A cikin hoton bidiyon da ya karade shafukan dandalin sada zumunta, an gano rikici ne ya kaure tsakanin yan jam'iyyar NPP da NDC kan wacce jam'iyya ne ke da rinjaye kuma wacce zata fitar da sabon Kakakin Majalisa.

Kamar yadda bidiyon ya nuna, wasu daga cikin yan majalisar sun rika kai wa juna hannu sannan wasu suka rika fatali da akwatunan kada kuri'a da ke zauren majalisar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164