Kakakin Buhari: Abin Da Ya Hada Ni Fada da Abba Kyari a Aso Villa Har Ya Rasu

Kakakin Buhari: Abin Da Ya Hada Ni Fada da Abba Kyari a Aso Villa Har Ya Rasu

  • Femi Adesina yace alaka ba tayi kyau tsakaninsa Abba Kyari a lokacin da yake aiki a Aso Villa ba
  • Mai magana da yawun na Muhammadu Buhari ya rubuta littafi a kan abubuwan da suka faru
  • Adesina ya bada labarin yadda shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ya kawo masu cikas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Femi Adesina wanda ya yi shekaru bakwai a matsayin mai magana da yawun Muhammadu Buhari ya rubuta littafi a kan mulkinsa.

A littafin da ya rubuta, Femi Adesina ya kawo maganar tsattsamar alakarsa da Marigayi Abba Kyari, Tribune ta kawo labarin da ke cikin littafin.

Femi Adesina da Abba Kyari
Femi Adesina da Abba Kyari Hoto: Femi Adesina, Bashir Ahmaad
Asali: Facebook

Mai magana da bakin shugaban Najeriyan a lokacin ya ce tun farko bai samu jituwa sosai da Abba Kyari ba, wanda ya rasu a dalilin COVID-19.

Kara karanta wannan

Jibrin dan Sudan: Mai daukan Buhari hoto ya magantu kan zargin sauya tsohon shugaban kasar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adesina ya ga katangar Abba Kyari

Adesina ya ce Abba Kyari bai yi na’am da yadda ya rika ganin shugaban kasa kai-tsaye ba duk da haka Muhammadu Buhari ya bada umarni.

Har zuwa lokacin da ya rasu, marubucin yace Marigayi Kyari ya hana su kudin da suke bukata wajen harkokin yada labarai a fadar Aso Villa.

Kyari ya hana Adesina daukar aiki

Duk da shugaban kasa ya amince ya dauki ma’aikata, marubucin yace Kyari ya hana hakan ta faru, amma wannan bai lalata dangatakarsu ba.

Rahoton New Telegraph yace Adesina ya yi kokarin nesanta kan shi da babban hadimin fadar shugaban kasar zuwa karshen alakarsu.

Duk da yadda abubuwa ba suyi dadi ba, tsohon ‘dan jaridar yace babu wanda ya isa ya yi shakkun amannar Kyari ga Muhammadu Buhari.

A littafinsa, mai magana da yawun tsohon shugaban yace a wurinsa duk wanda yake kaunar mai gidansa, ya yafe masa kowane irin laifi.

Kara karanta wannan

Yadda Shugaban kasa ya ba ni mukami bai taba gani na ba Inji Mai daukar hoton Buhari

Haka hadiman yace haka suka shafe shekaru babu kudi saboda shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ya ki amincewa da kasafinsu.

Yayin da COVID-19 ta kashe Malam Kyari, Adesina a littafinsa ya ce mutuwar ta taba shi.

Aiki da Muhammadu Buhari

Bayo Omoboriowo ya bada labarin yadda ya zama mai daukar hoton Muhammadu Buhari ba tare da yana da kafa a cikin fadar Aso Villa ba.

A cewar Bayo Omoboriowo, ya saida ruwa a kan titi kafin ya samu dauka a rayuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel