Abubuwa 4 masu rikitarwa game da mutuwar Abba Kyari

Abubuwa 4 masu rikitarwa game da mutuwar Abba Kyari

Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Abba Kyari ya rasu a ranar Juma'a amma an birne shi a safiyar ranar Asabar.

An birne shi ne a makabartar Gudu da ke Abuja amma kuma akwai wasu al'amura masu matukar rikitarwa game da mutuwarsa.

1. Hasashen Kemi Olunloyo: Tun bayan da mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman Femi Adesina ya tabbatar da mutuwar Kyari, sunan Kemi Olunloyo ya ci gaba da yawo a kafafen sada zumunta.

Kemi diyar tsohon gwamnan jihar Oyo ce wacce a cikin kwanakin nan ta bayyana cewa wani babban jami'in gwamnatin kasar nan ya rasu sakamakon Covid-19.

Duk da ba ta sanar da ko waye ba, ta ce jami'in ya rasu ne tun kafin ranar Juma'a. A lokacin kuwa Kyari ne kadai yake jinya sakamakon cutar.

Abubuwa 4 masu rikitarwa game da mutuwar Abba Kyari
Abubuwa 4 masu rikitarwa game da mutuwar Abba Kyari
Asali: Twitter

2. Shekarun haihuwar Kyari: Jim kadan bayan rasuwarsa, Wikipedia ta bayyana cewa yana cikin shekarunsa na 70 ne da doriya amma ba a bayyana ko nawa bane takamaimai.

Gidan talabijin na TVC kuwa ta bayyana cewa, an haifeshi ne a 1938 kuma ya rasu a 2020 wanda ke nufin shekarunsa 81.

Abubuwa 4 masu rikitarwa game da mutuwar Abba Kyari
Abubuwa 4 masu rikitarwa game da mutuwar Abba Kyari
Asali: Twitter

3. Asalin inda ya rasu: Ba kamar sauran mace-macen da ke faruwa sakamakon Covid-19 a Najeriya ba, har yanzu ba a bayyana inda Abba Kyari ya yi jinya ba har ya rasu.

Abu daya da aka sani shine ya rasu a jihar Legas.

Abubuwa 4 masu rikitarwa game da mutuwar Abba Kyari
Abubuwa 4 masu rikitarwa game da mutuwar Abba Kyari
Asali: Facebook

4. Karya dokar nisantar juna yayin birne shi: Kamar yadda hotuna da bidiyo suka bayyana, manyan kasar nan da suka sallaci gawar marigayin basu nisanci juna ba.

Hakazalika, har zuwa birne shi da aka yi a makabartar Gudu da ke Abuja, manyan jami'an gwamnatin Najeriya sun kasance masu cudanya da juna.

Abubuwa 4 masu rikitarwa game da mutuwar Abba Kyari
Abubuwa 4 masu rikitarwa game da mutuwar Abba Kyari
Asali: Twitter

Idan za mu tuna, a ranar 3 ga watan Afirilun 2020, Lai Mohammed ya tabbatar da cewa koda gawar wanda ya mutu sakamakon annobar ce, bai dace a kusance ba.

Ya bayyana cewa tana dauke da kwayoyin cutar kuma ana iya dauka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel