Takaitaccen tarihin marigayi Abba Kyari

Takaitaccen tarihin marigayi Abba Kyari

Abba Kyari haifaffen dan kabilar Kanuri ne daga jihar Borno da ke Arewa maso gabas din Najeriya. Ya samu karatun firamare da na sakandare a jihar Borno.

Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Warwick ta Ingila a fannin halayyar dan Adam a 1980.

Hakazalika, ya sake kammala wani digirin a fannin shari'a daga jami'ar Cambridge.

Ya zama lauya a shekarar 1983, bayan ya halarci makarantar horar da lauyoyi ta Najeriya.

A shekarar 1984, Kyari ya kammala digirinsa na biyu a fannin shari'a daga jami'ar Cambridge.

Daga baya, ya halarci kwalejin gudanarwa ta Lausanne da ke Switzerland a 1992.

Ya sake halartar horarwa a kan gudanarwa da ci gaban al'umma a makarantar koyar da kasuwanci ta Harvard a 1994.

Marigayin yayi aiki a wurare da dama. Ya yi aiki a matsayin edita a New Africa Holdings Limited da ke Kaduna daga 1988 zuwa 1990.

Ya zama kwamishinan Gandun daji da albarkatun dabbobi na jihar Borno a 1990.

Kyari ya zama sakataren kwamitin gudanarwa na African International Bank Limited daga 1990 zuwa 1995.

Kyari ya taba zama daraktan bankin UBA kafin daga bisani ya zama shugaban bankin.

An nada shi a matsayin daraktan Unilever Nigeria a 2002, kuma ya taba aiki da Exxon Mobil Nigeria.

Takaitaccen tarihin marigayi Abba Kyari
Takaitaccen tarihin marigayi Abba Kyari
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Shugaban ma'aikatan Najeriya Abba Kyari ya riga mu gidan gaskiya

Abba Kyari ya zama shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa a watan Augustan 2015.

A wannan matsayin da Kyari ya taka, yana da ruwa da tsaki a kan komai da ya shafi shugaban kasar.

Shi yake tsara komai game da ayyukan shugaban kasar sannan yana ganawa da a kalla mutum 20 a kowacce rana.

Kamar yadda wani dan jarida da ke aiki a fadar shugaban kasa ya bayyana, a kalla ya kan gana da shugaban kasa sau hudu a rana.

Hakazalika, yana ganawa da gwamnoni da ministoci tare da sauran manyan jami'an gwamnati masu bukatar ganawa da shugaban kasar.

Sakamakon wannan mukamin nashi, mutane da yawa na zarginsa da juya akalar gwamnatin kasar nan, lamarin da shugaban kasar ya musanta.

Abba Kyari ya rasu ya bar matar aure daya da 'ya'ya hudu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel