Yadda Shugaban Kasa Ya Ba Ni Mukami Bai Taba Gani Na ba Inji Mai Daukar Hoton Buhari
- Bayo Omoboriowo ya kawo tarihin haduwarsa da Muhammadu Buhari, wanda ya ba shi mukami a mulkinsa
- Matashin ya zama mai daukar hoton shugaban kasa a lokacin da bai da kusanci da manyan ‘yan siyasa
- Omoboriowo ya kware wajen harkar hoto, a dalilin haka APC ta dauke shi wajen daukar hotunan kamfe
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Bayo Omoboriowo shi ne mai daukar Muhammadu Buhari hoto a lokacin yana mulki, ya bada labarin yadda ya samu daukaka.
Bayo Omoboriowo bai san kowa ba, amma sai ga shi yana aiki a fadar shugaban kasa, shi bada labarin nan da Channels tayi hira da shi.
Kwararren mai hoton ya bayyana cewa ayyukan da ya yi a baya suka taimaka masa samun matsayi a mulkin Muhammadu Buhari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tarihin rayuwar Bayo Omoboriowo
Omoboriowo ya kafa MadHouse by Tikera kuma ya shahara wajen daukar hotuna, sai dai da farko yana aikin zaman kan shi ne a Najeriya.
Sannu a hankali har ya fara aiki da gidan BellaNaija, wannan ya kara masa shahara sosai. Vanguard ta fitar da rahoton hirar da aka yi.
A hirar da aka yi da shi a gidan talabijin, Omoboriowo yace ana haka sai wata rana wani ya kira shi daga Ingila domin yi wa wasu aiki.
Zuwa digiri a jami'ar Legas
Tun asali ya karanta ilmin sinadarai ne a jami’ar Legas, matashin yace a lokacin da ya gama hidimar kasa sai ya tafi koyon daukar hoto.
A lokacin ya rika rabawa ne a cikin dakin dalibai a jami'a domin koyon amfani da manhajar Photoshop har ya kware wajen gyara hotuna.
Wannan Bawan Allah yace ya taba zama mai saida ruwan leda a titunan Legas.
Da BellaNaija suka fara haska hotunansa sai ya yi suna a duniya, zuwa 2012 sai ga shi yana samun kyautattuka da kuma lambobin yabo.
A 2014 ya ga ana neman masu daukar hoto, ko kafin nan ya yi da Kayode Fayemi da Rauf Aregbesola, silar daukakarsa kenan a aikin.
Haduwar Omoboriowo da Muhammadu Buhari a 2014
Da aka je taron zaben ‘dan takaran APC a 2014, sai aka sacewa Omoboriowo wayarsa. Hakan bai hana shi nuna kwarewa da baiwarsa ba.
A hankali ya samu damar daukar hoton Muhammadu Buhari wajen kamfe, bayan APC ta ci zabe sai ya zama mai hoton shugaban kasa.
Auren dolen NNPP da APC a Kano
A babin siyasa, ana da labari shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nemi shugaban na APC ya fara aikinsa da yin sulhu da Rabiu Kwankwaso.
A matsayinsa na shugaban jam’iyya na kasa, ana bukatar Abdullahi Umar Ganduje ya jawo ‘yan adawa, a ciki har da jigon na NNPP.
Asali: Legit.ng