Daga Karshe An Bayyana Masu Daukar Nauyin Matsalar Rashin Tsaron da Ta Addabi Abuja

Daga Karshe An Bayyana Masu Daukar Nauyin Matsalar Rashin Tsaron da Ta Addabi Abuja

  • Ƙungiƴar ƴan Najeriya mazauna ƙasashen Amurka da Birtaniya (UNTF), ta yi magana kan rashin tsaro a Abuja
  • Ƙungiyar ta bayyana cewa masu adawa da ministan Abuja, Nyesom Wike ne ke ɗaukar nauyin matsalar rashin tsaron
  • Ta yi nuni da cewa masu wannna maƙarƙashiyar suna yin hakan ne domin kawo naƙasu a dangantakar da ke tsakanin Wike da Shugaba Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƴan Najeriya mazauna Amurka da Birtaniya ƙarƙashin inuwar ƙungiyar UNTF, reshen Arewacin Amurka sun yi magana kan matsalar rashin tsaron da ta addabi birnin tarayya Abuja.

Ƙungiyar ta danganta yawaitar laifuka a babban birnin tarayya Abuja, kan waɗanda ke adawa da dabarun cigaba na ministan Abuja, Nyesom Wike, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya sa labule da tawagar ƙungiyar kiristoci ta ƙasa CAN a Villa, bayanai sun fito

An fadi masu daukar nauyin rashin tsaro a Abuja
An bayyana masu daukar nauyin matsalar tsaro a Abuja Hoto: @govwike
Asali: Facebook

A cewar ƙungiyar ta UNTF, ɗimbin nasarorin da Nyesom Wike ya samu a babban birnin tarayya Abuja da ayyukan samar da ababen more rayuwa, ya sanya ake adawa da shi, rahoton The Sun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Su waye ke ɗaukar nauyin rashin tsaro a Abuja?

Sun kuma nuna cewa goyon bayan Wike ga Shugaba Bola Tinubu ne ya sa suka duƙufa wajen tada zaune tsaye da ɗaukar nauyin sace-sacen jama’a da rashin tsaro a Abuja don haifar da rashin jituwa tare da tarwatsa dangantakar da ke tsakanin Wike da Shugaba Tinubu.

Babban sakataren ƙungiyar Mista Kenneth Friday, a cikin wata sanarwa ya nuna damuwarsa kan yadda ake ci gaba da yin garkuwa da mutane a babban birnin tarayya Abuja.

Ya bayyana ƙwarin gwiwarsa kan ministan, shugaban ƙasa Tinubu da hafsoshin tsaro wajen shawo kan matsalar rashin tsaro.

Kara karanta wannan

Ana cikin matsalar rashin tsaro, ministan tsaro ya fadi abu 1 da ya kamata yan Najeriya su yi

Ƙungiyar ta kuma yi kira ga Sufeto-Janar na ƴan sanda, Kayode Egbetokun da ya gaggauta janye jami’an tsaro da suka wuce ƙima da ake ba ƴan siyasa tare da tura su cikin sabuwar rundunar tsaron da aka kafa don magance tsaro a Abuja.

Majalisa Za Ta Gayyaci Wike

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Ireti Kingibe ta ce majalisar dattijawa za ta gayyaci ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike da hukumomin tsaro.

Sanatan mai wakiltar birnin tarayya Abuja ta bayyana cewa majalisar za ta gayyace su ne kan yawaitar ayyukan ƴan ta'adda a babban birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel