Abun al’ajabi: An haifi jariri dauke da Kur’ani da carbi a jihar Bauchi

Abun al’ajabi: An haifi jariri dauke da Kur’ani da carbi a jihar Bauchi

A kullun abubuwan al’ajabi suna ci gaba da faruwa inda Allah ke nuna buwayarsa wanda hakan kukan kurciya ne ga mai hankali da tunani.

Hakan ce ta kasance a jihar Bauchi lokacin da wata baiwar Allah ta haifi yariri dauke da al-Kur’ani da kuma carbi a hannunsa.

A lokacin da matar ta iso da labarin mai cike da al'ajabin zuwa gidan Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ta byyana cewa, haka ta haifi yaron wanda aka rada masa suna Muhammad Auwal. Ta kuma rantse da Allah cewa wannan lamari gaskiya ne babu kokonto.

A yayain hadubar Juma'ar da ta gabata da Sheikh Dahiru Bauchi ya yi, ya ce "wannan ba komai bane a wurin Ubangiji illah raddi ga kafurai masu inkari da Annabi (SAW), don kara nuna musu cewa Manzon Allah gaskiya ne.

"Sannan ya kara nuna wa duniya irin mu'ujizar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam. Shine ya sa aka haifo wannan yaro da Kur'ani da kuma carbi".

Shehin Malamin ya kara da cewa "wannan carbi kuma ba komai bane face raddi ne ga masu inkarin Shehu Tijjani da darikarsa ta Tijjaniyya, don Allah ya kara nuna wa duniya cewa Dariku gaskiya ne.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya rattaba hannu kan yarjejeniya da kasar Switzerland kan dawo da kudaden Najeriya

Shehin ya kara da cewa duk ga alamomin Tijjaniyya a jikin wannan carbin. Wannan karamar Shehu Tijjani ne ta kara bayyana ga masu inkarin me Darikar ta Tijjaniyya.

A karshe Shehin ya yi addu'ar Allah ya kare Musulunci Da Musulmai, ya kuma zaunar da Nijeriya lafiya tare da kare ta daga dukkan bala'o'i.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng