Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Tawagar Ƙungiyar Kiristoci Ta Kasa CAN a Villa, Bayanai Sun Fito

Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Tawagar Ƙungiyar Kiristoci Ta Kasa CAN a Villa, Bayanai Sun Fito

  • Bola Ahmed Tinubu ya gana da shugabannin ƙungiyar kiristoci ta ƙasa CAN a fadar shugaban ƙasa da ke birnin tarayya Abuja
  • Duk da Tinubu ya lashe zaben shugaban ƙasa da tikitin Musulmi da Musulmi, ya yi alƙawarin kafa gwamnatin kowa da kowa
  • Har yanzu babu cikakken bayani kan makasudin wannan taro amma dai ya zo ne kwanaki kaɗan bayan Tinubu ya gana da tawagar majalisar shari'ar musulunci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaba ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya gana da shugabannin kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) a fadar gwamnati da ke Abuja ranar Litinin, 22 ga watan Janairu.

Wannan shi ne taro na farko a sabuwar shekara 2024 tsakanin shugaba Tinubu da ƙungiyar mabiya addinin kirista ta Najeriya, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Daga karshe an bayyana masu daukar nauyin matsalar rashin tsaron da ta addabi Abuja

Shugaba Tinubu ya gana da CAN.
Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Shugabannin CAN a Fadarsa Da ke Abuja Hoto: Ajuri Ngelale
Asali: Facebook

Legit Hausa ta fahimci cewa wannan ganawa na zuwa ne kwanaki ƙalilan bayan majalisar ƙoli ta shari'ar Musulunci a Najeriya (SCSN) ta gana da Tinubu a Villa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manyan malaman musuluncin sun yaba da tsare-tsaren Bola Tinubu kan batun tattalin arzikin ƙasa kana suka nemi ya ƙara dagewa wajen kawo karshen matsalar tsaro, Guardian ta rahoto.

Wannan tattaunawa da shugaban ƙasar ke yi da manyan shugabanni a Najeriya na zuwa ne a daidai lokacin da sha'anin tsaro ke ƙara taɓarbarewa.

Tinubu ya gana da hafsoshin tsaro

Idan baku manta ba, Shugaba Tinubu ya gana da manyan hafsoshin tsaron ƙasar nan a fadar shugaban ƙasa kan batun yanayin tsaro da ke ƙara munana a sassan Najeriya.

Babban hafsan tsaron ƙasa, Janar Christopher Musa da shugaban rundunar sojojin ƙasa, Laftanar Janar Taoheed Lagbaja na cikin waɗanda suka halarci wannan zama.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya taya jigon PDP murnar zagayowar ranar haihuwarsa, ya fadi kyakkyawan halinsa

Taron ya gudana ranar Talata, 16 ga watan Janairu, 2024 yayin da hare-haren ƴan ta'adda ke ƙara yawaita a faɗin ƙasa musamman babban birnin tarayya Abuja.

Gwamnan APC ya gana da masu ruwa da tsaki

A wani rahoton kuma Gwamna Aiyedatiwa ya gana da masu ruwa da tsakin jam'iyyar APC karo na farko bayan hawa mulkin jihar Ondo.

Da yake jawabi a wurin, ya buƙaci jagororin APC mai mulki su haɗa kai kuma su zauna lafiya da juna gabanin zaben gwamna mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel