Zargin Cin Hanci: EFCC Za Ta Binciki ‘Dan Siyasar Da Ya Fi Kowa Dadewa a Majalisa
- Babban kotun tarayya da ke aiki a Abuja ta gamsu hukumar EFCC ta yi shari’a da Nicholas Mutu
- Ana tuhumar ‘dan majalisar da cin wasu kudi a lokacin da ya rike shugabancin kwamitin NDDC
- A watan gobe Hon. Mutu zai kare kan shi a kotu, haka zalika kamfanoni biyu da ake zargi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Babban kotun tarayya mai zama a garin Abuja ta ki amincewa da wani roko da Nicholas Mutu ya gabatar a gabanta.
Rahoton The Nation ya ce kotun tarayyar ta ki amincewa Nicholas Mutu ya hana a binciki shi da wasu a kan zargin cin kudi.
EFCC za ta hadu da Mutu a kotu
Ana zargin fitaccen ‘dan siyasar tare da kamfanonin Airworld Technologies Ltd da Oyien Homes Ltd wajen badakalar N320m.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutu yana wakiltar mazabar Bomadi/Patani daga jihar Bayelsa a majalisar wakilan tarayya tun 1999, ya shekara 24 a kujerar.
Mai shari’a Folashade Giwa-Ogunbanjo ta gabatar da hukunci yau Litinin, ta ce akwai bukatar a binciki wadanda ake tuhuma.
An rahoto Folashade Giwa-Ogunbanjo tana cewa Nicholas Mutu da sauran wadanda ake zarhi su shirya kare kan su gaban kotu.
Zargi 13 su ke kan ‘dan majalisar tarayyan da wadannan kamfanoni, kuma kotu tace akwai hujjojin da ke nuna bukatar yin shari’a.
An tsaida lokacin shari'a da EFCC
Bayan zartar da wannan hukunci sai kotu ta daga zama zuwa 21 da 22 ga watan Fubrairu domin jin ta bakin lauyoyin bada kariya.
Hukumar EFCC ta shigar da wannan kara mai lamba FHC/ABJ/CR/123/2019 a kotun bisa zargin da ake yi wa Mutu a 2014 zuwa 2016.
Zargin da ake yi wa Mutu a kotu
Lauyoyin EFCC sun ce a lokacin yana shugaban kwamitin NDDC, ‘dan majalisar ya boye batun N320,159, 689 da aka biya wani kamfani.
Zargin da EFCC ta ke yi shi ne ‘dan majalisar ya yi amfani da kujerarsa, ya karbi cin hanci daga wani da aka ba kwnagila a Neja Delta.
Siyasar Kano sai Kano
Ana da labari Bola Tinubu ya nemi Abdullahi Ganduje ya garzaya ayi sulhu da Rabiu Kwankwaso wanda jigo ne a jam'iyyar NNPP.
A taron da shugaban kasa ya yi da jagororin APC, ya umarci ‘yan jam’iyya mai-mulki a Kano su shiga zawarcin madugun Kwankwasiyya.
Asali: Legit.ng