Kotu ta dage shari’ar da ake yi tsakanin wasu ‘Yan takara da APC kan zaben shugabannin Jam'iyya a Katsina

Kotu ta dage shari’ar da ake yi tsakanin wasu ‘Yan takara da APC kan zaben shugabannin Jam'iyya a Katsina

Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa Kotu ta sa rana domin koma zaman da ake yi da INEC da Jam’iyyar APC inda ake shari’a game da zabukan da APC tayi a cikin Jihar Katsina kwanakin baya.

Kotu ta dage shari’ar da ake yi tsakanin wasu ‘Yan takarar Gwamna da APC a Katsina
Wasu sun maka Hukumar INEC da Jam’iyyar APC kara a Kotu
Asali: Depositphotos

Babban Kotun Tarayya da ke zama a Birnin Abuja zai cigaba da zama a Ranar 8 ga wannan Watan domin cigaba da shari’ar da ake yi da Hukumar zabe na kasa da Jam’iyyar APC mai mulki game da wadanda aka ba shugabancin Jam’iyyar a Katsina.

Alkali mai shari’a Folashade Giwa ta dage karar ne a dalilin rashin isassun hujjoji daga wajen Hukumar zabe. Wasu masu neman kujerar Gwamna a APC ne su ka kai kara Kotu su na neman Kotu ta wargaza duk zabukan da APC tayi kwanakin baya.

KU KARANTA: Babban Kotun Najeriya ta wargazawa Jam’iyyar APC lissafi a Ribas

Garba Sani Dankani da Muhammad Sada Mainasara wanda su ke neman kujerar Gwamnan Katsina a APC sun nemi Alkali Folashade Giwa-Ogunbanjo ta soke zabukan da Jam’iyyar ta gudanar a Watan Mayu inda aka tsaida shugabannin Jam'iyya.

Babban Lauya Ola Olanipekun wanda shi ne kare masu karar yana neman Hukuma ta dakatar da duk shugabannin Kananan Hukumomi da kuma na Gundumomi da aka zaba a karkashin Jam’iyyar domin zaben da aka yi ya saba dokar kasa da tsarin Jam’iyya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng