A je a Sasanta da Kwankwaso: Sirrin Taron Ganduje, ‘Yan APC da Tinubu Sun Fito Fili
- Bola Ahmed Tinubu ya nemi shugabannin APC da ke jihar Kano suyi sulhu da abokan hamayyarsu
- Shugaban kasan ya gana da jiga-jigan jam’iyya mai mulki bayan an tabbatar da mulkin NNPP a Kano
- Idan zancen ya tabbata, za a tilastawa Abdullahi Umar Ganduje hada-kai da Rabiu Musa Kwankwaso
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya bukaci shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya sasanta da Rabiu Musa Kwankwaso.
Mai girma shugaban kasar ya yi wannan kira ne bayan an kammala shari’ar Kano a Kotun koli, Politics Digest ta fitar da labarin nan.
Tinubu ya ce Ganduje ya jawo Kwankwaso
Bola Ahmed Tinubu yana so Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya jawo duk wasu wadanda suke sha’awar shigowa jam’iyyar APC mai-ci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban Najeriyan ya bukaci dukkanin masu ruwa da tsaki a APC ta reshen jihar Kano su dinke duk wata baraka da ke tsakaninsu.
Bola Tinubu yana so ayi sulhu da daidaiku, kungiyoyi da duk wata jam’iyyar siyasa domin ganin an tafiyar da APC da jihar Kano gaba.
Wannan umarni da shugaban kasa ya bada a wajen taron da aka yi da ‘yan jam’iyyar APC ya girgiza wadanda aka yi zaman tare da su.
Shugaba Tinubu ya kebe da jagororin APC a karkashin tsohon gwamna Abdullahi Ganduje domin ganin an tafiyar da jam’iyya gaba.
Kwankwaso?: 'Yan APC sun yi gum!
Jaridar da ta kadaita da rahoton ta ce Tinubu ya nemi jin ta bakin ‘yan APC na Kano ko akwai wani wanda yake da ja da matsayarsa.
Daukacin wadanda aka yi zaman da su a Aso Rock Villa sun nuna sun bi umarnin shugaban kasa na sasantawa da abokan gaba.
Ina makomar Gawuna a APC?
Wani daga cikin jiga-jigan APC da ke wajen zaman ya nemi a ba Nasiru Yusuf Gawuna mukami, lamarin da ya fusata shugaban kasa.
Majiyarmu ta shaida mana Mai girma Tinubu bai ji dadi da aka yi masa maganar jawo ‘dan takaran gwamnan a zaben jihar Kano ba.
Wani 'dan siyasa ya fada mana shugaban kasa ya tunawa Ganduje cewa ya san Kwankwaso a 1992 kafin ya hadu da shi bayan 1999.
A cewarsa, Mai girma Tinubu ya nunawa shugaban jam'iyyar yadda yake bukatar karin masoya a maimakon abokan gaba a siyasarsa.
Abba, Kwankwaso za su dawo APC?
Da wannan umarni na shugaban kasa, an fara maganar sulhu da gwamna Abba Kabir Yusuf wanda Kotun koli ta tabbatar da kujerarsa.
Shugabannin NNPP a Kano sun bukaci lokaci su tattauna da jagoransu na kasa, Rabiu Musa Kwankwaso kafin su iya yanke hukunci.
Idan hakan ta faru, watakila NNPP ta samu rabin mukaman jam’iyya a jihar Kano. Gidan rediyon Express ta fitar da makamacin labarin.
"A kawo Kwankwaso, kori Ganduje" - Matasan APC
Ana da labari wasu da sunan matasan APC sun fara huro wuta a tsige Abdullahi Umar Ganduje kuma a hana shi mukami a gwamnati.
Kungiyar ta roki a dauke Rabiu Kwankwaso daga jam’iyyar NNPP, a dawo da shi APC.
Asali: Legit.ng