Cin hanci: EFCC ta kama shugaban kwamitin majalisar wakilai mai kula NDDC

Cin hanci: EFCC ta kama shugaban kwamitin majalisar wakilai mai kula NDDC

Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) ta gurfanar da shugaban kwamitin majalisar wakilai mai kula da hukumar habaka yankin Neja Delta, Nichold Mutu, a gaban wata babbar kotun tarayya dake Abuja.

An gurfanar da Mutu ne a gaban kotun sakamakon zarginsa da hannu a wata badakalar kudi har naira miliyan dari hudu tare da kuma karbar wasu kudin daga hannun 'yan kwangila a yankin, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Mutu wanda ya kasance shugaban kwamitin majalisar wakilan mai kula da hukumar habaka yankin Neja Delta din tun shekarar 1999, ya musanta aikata abinda ake zarginsa da shi.

Cin hanci: EFCC ta kama shugaban kwamitin majalisar wakilai mai kula NDDC
Cin hanci: EFCC ta kama shugaban kwamitin majalisar wakilai mai kula NDDC
Asali: UGC

Mai shari'a Folashade Giwa-Ogunbanjo ya bukaci wanda ake zargin da ya ci gaba da harkokinsa tun da an riga an bayar da belinsa a kwanakin baya.

DUBA WANNAN: Babbar magana: Wani miji ya like al'aurar matarsa da 'super glue' don kar ta ci amanarsa

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, wani magidanci ya yanke shawarar like gaban matarsa bayan da ya gano tana bin maza a duk lokacin da ya bar gari don harkokin kasuwancinsa.

Dennis Mumo, babban mutum ne da ake ganin kimarsa a Kitui. Son da yake wa matarsa ne da rashin son rabuwa da ita ne yasa ya like gabanta da sufa gulu har zuwa ranar da zai dawo daga balaguron kasuwancinsa.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, a ranar Juma'a ne aka kama Dennis da laifin wannan aikin da yayi a kan matarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng