Budurwa Ta Koka Bayan Ta Ci Karo da Shinkafa a Cikin Cincin Din ‘Mitifie’ da Ta Siya a Legas

Budurwa Ta Koka Bayan Ta Ci Karo da Shinkafa a Cikin Cincin Din ‘Mitifie’ da Ta Siya a Legas

  • Wata matashiya yar Najeriya ta garzaya soshiyal midiya don nuna abun da ta gano a cikin cincin din 'mitifie' da ta siya a wani garejin mota
  • A cikin wani bidiyo da ya yadu, an raba 'mitifie' din gida biyu don nuna cikinsa wanda je kunshe da shinkafar dafa-duka
  • Yayin da mutane da dama suka yi mata ca a ka na son ganin abun arziki a cincin din da ta siya N50, abun ya ba wasu dariya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta koka a soshiyal midiya bayan ta gano shinkafar dafa-duka a cikin cincin din 'mitifie' da ta siya N50.

Ta garzaya dandalin TikTok don baje kolin cincin din da abun da ya kunsa a ciki.

Kara karanta wannan

"Kan mijina kato ne sosai": Mata mai juna biyu ta shiga zullumi yayin da lokacin nakudarta ya gabato

Budurwa ta ga shinkafa a cikin mitifie
Budurwa Ta Koka Bayan Ta Ci Karo da Shinkafa a Cikin Cincin Din ‘Mitifie’ da Ta Siya a Legas Hoto: @theabisola
Asali: TikTok

Bidiyon matar mai tsawon sakan shida ya nuna cewa ta siya mitifie din ne a wani garejin mota a Legas. A daidai lokacin kawo rahoton nan, bidiyon nata ya samu mutum fiye da 199k da suka kalla.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutane da dama sun yi caa a kan matashiyar, suna mamakin ko tana tsammanin ganin abun da ya yi kasa daga abun da aka siyar mata a kan wannan farashin.

Wasu kuma sun bayyana cewa irin haka ya taba faruwa da su.

Kalli bidiyon a kasa:

Mutane sun bayyana ra'ayinsu

Danny ta ce:

"Ina ganin ya kamata ki siya karin wasu sannan sai ki cire shinkafar ki ci shinkafar ita kadai."

Goddess_angel ta ce:

"Shin ni kadai ce nake tsoron siyan mitifie kan 200....ranar da wani mutumi ya fa mun mitifie dinsa 100# ce ban yarda na siya ba fa. Na zo na ga dankalin turawa kawai a ciki."

Kara karanta wannan

Tsige yan majalisar PDP 23: Gwamnan Filato ya ziyarci Tinubu, ya yi karin bayani

promise tylor ta ce:

"Ni dai ba zai iya ci gaba da biyewa ba, nice nake siyar da wannan fulawar mai shinkafa."

Prazido ta ce:L

"Kin siya kan 50 naira, me kike tsammanin gani a ciki."

SASBOY ya ce:

"Da naira 50? Miyan kubewa ya kamata a gani a ciki."

Yadda bature ya ji dadinsa da dala 1

A wani labarin, mun ji cewa wani bature mai suna Chris wanda ke yin bidiyoyi masu kayatarwa kan Najeriya da mutanenta ya sake yin wani.

A sabon bidiyon, mutumin ya canja kudi dala daya sannan kudin ya kama N900 da aka mayar da shi naira. Ya yi amfani da kudin wajen more rayuwa a gari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel