Wata Mata Ta Bayyana Yadda Ta Haihu a Asibiti Ba Ta Sanin Ta Na Dauke da Ciki Ba

Wata Mata Ta Bayyana Yadda Ta Haihu a Asibiti Ba Ta Sanin Ta Na Dauke da Ciki Ba

  • Wata mata ta bayyana yadda ta je asibiti don neman maganin ciwon ciki amma a karshe ta haifi ‘yarta jaririya
  • Matar mai suna Favour ta ce ta fara fuskantar yawan kiba yayin da daga bisani ta koma kawadayin komai da ta gani
  • Mutane da dama sun yi martani inda su ke cewa yanzu ana yawan samun irin wannan juna biyun a jikin mata

Wata mata ‘yar Najeriya mai suna Favour Ehizibue ta bayyana yadda ta gamu da juna biyu mai dauke da abin al’ajabi.

Matar ta yada faifan bidiyo a TikTok inda ta ce ta je asibiti neman maganin ciwon ciki amma abin mamaki ta dawo gida da jaririya.

Mata ta haihu a asibit ba tare da sanin da ta na dauke da ciki ba
Wata mata ta bayyana yadda ta haihu ba tare da ta san ta na ciki ba. Hoto: @favourofafrica_.
Asali: TikTok

Favour ta ce bata taba sanin ta na da juna biyu ba lokaci daya kawai ta ga alamun ta na kara kiba wanda hakan ya saka ta yi murna.

Kara karanta wannan

Ana ta 'rushing': Budurwar ta tashi kan samari da kitso diban baya, ta yada bidiyo

Yawan kiban nata ya saka ta na jin kwadayin abubuwa inda ta ke fama da kumburar fuska ta dauka cewa kawai matsalar fatar jiki ce, Legit ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce a karshe, ta yi fama da ciwon ciki wanda duk a daukanta magani kawai ta ke bukata amma da zuwanta asibiti sai aka shigar da ita dakin haihuwa.

Ku kalli bidiyon a kasa:

Mutane da dama sun yi martani kan wannan lamari na matar:

Slays_hub:

“Ni ma ina fama da irin wannan matsalar, ina cin abinci sosai kuma kwadayi na ya karu.”

A love:

“Ban da ni kam, ina fama da duk abin da kika fada, ubangiji ka tsare ni.”

Olakiitan:

“Kullum sai na taba tumbi na saboda kada wani jariri ya ba ni mamaki saboda ban shirya ba.”

Kara karanta wannan

Rahin Tausayi Yayin da Mata Ta Babbaka Dan Kishiyarta da Dutsen Guga Kan N200, Ta Koka Kan Halin Yaron

Jossyalbie:

“Ubangiji na yin haka saboda ya san mutane za su ki karbar kyautar da ya yi musu, yanzu ana yawan samun irin wannan juna biyun.”

Meme Goddess:

“Ina yawan jin labarin irin wannan cikin, ina jin tsoro sosai saboda ban yi bako ba har yanzu.”

Eucharia:

“Me yasa ake yawan samun irin wannan cikin yanzu, ya yi yawa a gari.”

Matashi ya dirka wa mata 3 'yan gida daya ciki

A wani labarin, An bayyana yadda wani matashi wanda ba a bayyana sunan shi ba wanda ya ke kula da lambu ya lallaba wasu ‘yan mata uku ‘yan gida daya tare da dirka musu ciki gaba dayansu.

Rahoton da mu ka gani wanda aka yada a kafar Facebook ya tabbatar cewa matashin ya dirka wa mata uku 'yan gida daya duk da kula da su da iyayensu ke yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.