Ranar da Jirgin Shugaban Kasa Ya Kusa Kifewa da Buhari da Hadimansa a 2015

Ranar da Jirgin Shugaban Kasa Ya Kusa Kifewa da Buhari da Hadimansa a 2015

  • Muhammadu Buhari ya ga ta kan shi a lokacin da jirginsa yake hanyar zuwa kasar Malta a shekarar 2015
  • Ba a dade da hawa mulki ba, shugaban Najeriyan ya shirya tafiya wajen taron kasashen renon kasar Birtaniya
  • Femi Adesina a littafin da ya rubuta kwanan nan, ya ce jirgin shugaban kasa ya yi tangal-tangal aka gaza sauka

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Jirgin da ya dauko Muhammadu Buhari ya kusa yin hadari dauke da mukarrabansa lokacin da yake karagar mulki.

Vanguard ta kawo rahoton wannan abin da ya faru a Nuwamban shekarar 2015 kamar yadda ya zo a littafin tarihin shugaban.

Buhari jirgi
Muhammadu Buhari a jirgin shugaban kasa Hoto: @drwalls28
Asali: Twitter

Femi Adesina ya rubuta littafi dauke da tarihin abubuwan da suka faru a lokacin da Muhammadu Buhari yake mulkin kasar nan.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da ganawa kan matsalar tikitin Musulmi da Musulmi, Tinubu ya nada dan Arewa babban mukami

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buhari ya yi shekaru takwas a ofis tsakanin 2015 da 2023 kafin zuwan Bola Tinubu.

Jirgin Buhari a hanyar zuwa Malta

Kamar yadda Femi Adesina ya rubuta a littafin na sa, jirgin ya dauko Muhammadu Buhari ne da nufin halartar taro a tsibirin Malta.

An shirya Mai girma shugaban Najeriya na lokacin zai yi zama da sauran kasashen renon Birtaniya, sai aka samu matsala a hanya.

Adesina wanda ya yi aiki da Buhari ya ce jirgin ya rika jijjiga a sararin samaniya na tsawon lokaci kafin matuka su shawo kan abin.

Hankalin Buhari ya tashi a jirgin sama

Hadimin ya ce da jirgin shugaban kasan ya yi wani sauka maras dadi a Malta, sai da ta kai Buhari ya tambayi abin da yake faruwa.

Jaridar ta ce a nan mai tukin jirgin ya ba shugaban kasa da sauran ‘yan ayarinsa hakuri ganin yadda hankalin tsohon sojan ya tashi.

Kara karanta wannan

Gyadar dogo: Mutanen da suka sha da kyar da aka kifar da Gwamnatin Najeriya a 1966

Jirgin shugaban kasa bai fi karfin matsaloli irin wannan ko na yanayin hazo ba, matukin jirgin ya shafe tsawon awanni yana tangadi.

Tafiye-tafiyen Muhammadu Buhari

Marubucin littafin ya ce an bada sanarwa jirgin na Boeing 737 zai sauka, daga nan aka gamu da tasgaro saboda canzawar kadawar iska.

Littafin ya ce tsohon shugaban kasar ya yi tafiye-tafiye fiye da 50, ya ziyarci kasashe 94

Wole Soyinka zai yi fallasa

Ana da labari Farfesa Wole Soyinka ya ce nan gaba zai fito da sunayen wasu a gwamnatin Bola Tinubu da ba su da gaskiya.

Idan ya fallasa wadanda ake zargi ba su da gaskiya, dattijon zai so hukumomi suyi ram da su duk da suna cikin jam’iyya mai mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel