Femi Adesina Ya Bayyana Makiyan Tsohon Shugaban Kasa, Buhari Guda 3 Lokacin Mulkinsa

Femi Adesina Ya Bayyana Makiyan Tsohon Shugaban Kasa, Buhari Guda 3 Lokacin Mulkinsa

FCT, Abuja - Femi Adesina, kakakin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana kalubalen da mai gidansa ya fuskanta a lokacin mulkinsa

Adesina ya bayyana haka yayin wata ganawa da manema labarai a jiya Laraba 20 ga watan Satumba a Osogbo babban birnin jihar Osun.

Femi Adesina ya bayyana makiyan Buhari 3 a gwamnatinsa
Femi Adesina Ya Yi Martani Kan Makiyan Gwamnatin Buhari. Hoto: Femi Adesina.
Asali: Facebook

Meye Femi Adesina ya ce kan makiyan Buhari?

Femi Adesina ya bayyana cewa Buhari ya fuskanci kalubale da dama daga makiyansa wadanda ke kawo cikas a gwamnatin.

Adesina ya ce a lokacin gwamnatinsu, Buhari ya hadu da manyan makiya guda uku da su ka kawo cikas a gwamnatin, Legit ta tattaro.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jerin wadanda su ka bai wa tsohon shugaban kasa, Buhari ciwon kai a mulkinsa:

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban Kasa Buhari Ya Yi Danasanin Wasu Abubuwa Da Ya Aikata a Kan Mulki, Bayanai Sun Fito

1. Jam'iyyar PDP

Adesina ya ce jam'iyyar PDP na daga cikin wadanda su ka mayar da hannun agogo baya a lokacin mulkinsu.

Ya ce duk da hakan za a iya kiransa adawa amma sun wuce gona da iri ganin yadda su ke kalar adawar ta su, Vanguard ta tattaro.

2. Wasu coci-coci

Femi ya ce coci da dama a kasar na jin haushi yadda aka kwace mulki a hannun tsohon shugaban kasa, Dakta Goodluck Jonathan.

Ya ce mafi yawan coci a Najeriya sun caccaki gwamnatin Buhari saboda kabilanci na addini.

3. Na hannun daman Buhari

Tsohon kakakin ya ce mafi yawa daga cikin wadanda Buhari ya nada mukamai ba su yi abin da ya dace ba a lokacin.

Ya kara da cewa Buhari ya yi yaki da cin hanci a kasar da kuma shawo kan matsalar tsaro a yankuna da dama.

Kara karanta wannan

Yadda Likita Ya Yanke Jiki Ya Mutu Bayan Ya Shafe Tsawon Awanni 72 Yana Aiki a Asibitin LUTH

Ya ce daga zuwansu gwamnati ya fahimci makiyan gwamnatin Buhari da su ke kawo cikas.

Buhari ya yi nadamar wasu ayyuka a baya

A wani labarin, kakakin tsohon shugaban kasa, Femi Adesina ya ce Muhammadu Buhari ya yi dana sanin wasu ayyuka a lokacin mulkinsa.

Adesina ya bayyana haka ne a jiya Laraba 20 ga watan Satumba yayin wani taro a birnin Osogbo na jihar Osun.

Ya ce Buhari kafin ya sauka daga mulki ya ba shi dama har tsawon sa'o'i biyu don masa duk tambayar da ya ke so, kuma ya yi masa dai-dai gwargwado.

Asali: Legit.ng

Online view pixel