Yan Bindiga Sun Tafka Sabuwar Ta'asa Cikin Dare a Jihar Neja

Yan Bindiga Sun Tafka Sabuwar Ta'asa Cikin Dare a Jihar Neja

  • Al'ummar ƙauyukan Garam da Zhibi na ƙaramar hukumar Tafa dake jihar Neja sun shiga jimami kan ta'asar da ƴan bindiga suka tafka musu
  • Wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da bindigu sun kai hare-hare daban-daban a ƙauyukan inda suka sace mutum 17
  • Kwamandan ƴan banga na Garam ya tabbatar da cewa ƴan bindigan sun riƙa shiga gida-gida suna ɗaukar bayin Allah

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Wasu ƴan bindiga, a wasu hare-hare guda biyu a jiya Talata, sun yi garkuwa da mutum 17 daga garin Garam da kuma ƙauyen Zhibi da ke ƙaramar hukumar Tafa a jihar Neja.

Garam, inda aka yi garkuwa da mutum 14, yana kan hanyar Sabon-Wuse-Bwari, yayin da Zhibi, inda aka yi garkuwa da wasu mutum uku, wani ƙauye ne da ke da iyaka da ƙauyen Dei-Dei, wanda ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Bwari ta babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fadi hanya 1 da zai bi wajen magance matsalar rashin tsaro a Najeriya

Yan bindiga sun sace mutum 17 a Neja
Yan bindiga sun yi awon gaba da mutum 17 a Neja Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce wani kwamandan ƴan banga a Garam, Dantani Daniel, ya ce ƴan bindigan sun kai hari a unguwar Sabon-Unguwa da ke garin da misalin ƙarfe 1:00 na dare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daniel ya ƙara da cewa:

"Sun kwashe mutanen ne daga gidaje daban-daban sannan suka bar garin cikin ƙasa da sa'a guda."

Wani mazaunin garin ya ce maharan sun kai hari gidan wani ɗan sanda da ke zaune a unguwar inda suka harbe shi, cewar rahoton Allnews.

A cewarsa:

"An garzaya da shi babban asibitin Kubwa inda yake karɓar magani."

Ƴan bindiga sun sace ɗaliban jami'a

Wasu ɗalibai biyu mata na jami'ar Al-Qalam dake jihar Katsina sun faɗa hannun ƴan bindiga bayan sun yi garkuwa da su.

Ƴan bindigan dai sun yi awon gaba da ɗaliban waɗanda suka fito daga jihar Neja lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa makaranta.

Kara karanta wannan

Atiku ya bayyana abin da ya hana kawo karshen matsalar tsaro a kasar nan, ya fadi mafita

Gwamna Alia Ya Magantu Kan Sace Shugaban Ƙaramar Hukuma

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya yi martani kan sace muƙaddashin shugaban ƙaramar hukumar Ukum da ƴan bindiga suka yi.

Gwamna Alia ya buƙaci ƴan bindigan da su gaggauta sakinsa ba tare da sanya wani sharaɗi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng